Hauwau Kulu Yar Cikin Badala Hausa Novel
Bayan an zauna an nutsu, ta karbi lasifika ta fara da rero godiya ga duk mahalarta taron, da sauran zaqaquran lauyoyi ‘yan uwanta,
Duk da cewa wannan karon ma da bakin gilashin nata a idanunta. Hakan bai boye zahirin cikar zatinta da cikar kamalarta da iya adonta ba.
da kungiyoyin da suka hada mata wannan muhimmin taron gani da ido da gaisawa, kungiyoyin ne masu tabbatar da cewa,
mutane masu bukata ta musamman sun samu rabauta daga duk wani matsatsi na rayuwa karkashin tallafin *Sustainable Development Goals* da take yi wa aiki, ta sake godewa kungiyoyin nan da suka roki ta fito yau, duniya ta ganta,
kasancewar muryarta kadai aka sani a kafafan sadarwa, sun roki ta baiwa al’umma labarin ta, maiyuwuwa ya zamo *inspiration* ga al’ummar da suka samu kansu cikin kwatankwacin irin *situation* dinta.