Lokacin da za mu mutu babu wanda zai sani’: Labarai daga Gaza
Lokacin da za mu mutu babu wanda zai sani’: Labarai daga Gaza
Mutum hudu a Gaza sun naɗarwa BBC yadda rayuwa take kasancewa a lokacin da ake ruwan bama-bamai, suka yi bayanin yadda suke kwashe yini wajen neman abinci da ruwan sha da daddare kuma su yi ta fama da wajen fakewa daga harin sama, suna addu’ar ganin safiya ta gaba.
Tun ranar 7 ga watan Oktoba dakarun Isra’ila ke yi wa Zirin Gaza luguden bama-bamai, sun kashe Falasɗinawa sama da 10,000, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana.
Sun ce hare-haren dai na ramuwa ne kan wanda Hamas ta kai wa Isra’ila, wanda ya kashe sama da mutum 1,400 kuma aka kwashi 242 a matsayin garkuwa.
Rashin intanet da network ɗin wayar salula mai kyau yasa ba a jinhalin da ake ciki akai-akai, amma mutanen da muke da su a Gaza suna aiko mana sakonni da bidiyoyi lokacin da dama ta samu.
domin sayan data mai sauki
www.forfo