NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Kawai matar taci gaba da fad’ar, “yo in banda kin rai nani kin mayar dani ba’a bakin komai ba, dan bani ce na haife kiba, aini matar uban ki ce, kuma dolene na saka ki aiki kiyi mani, ko dan kin ga uban naki baya a raye ne iye? “.

Masifar tace ta ishe ni nace, “dan Allah Mama kiyi hakuri ki dubi halin da nake ciki ki dubi yanda nayi kumburi bayana ciwo yake yi mani gashi daket nake zama daket nake tashi, kuma fa ɗazun inno ta sakani wankin yara da nata kayan wallahi da zaune na ƙarasa shi ma”.

Cike da jin zafin maganar da take sakar mani mai mugun ƙona mani zuciya jin na keyi da sa’a tace ba matar ubana ba wallahi da duk irin yanda nake jin jiki na sai na mareta, kawai nace da ita, “Ai kuwa wallahi a yanda nake jin nan ba zan iya yi maki wani abun ba, da ƙasan ciki na ma ciwo yakeyi da baya na! “.

Hannu wa Mama ta fara tafawa tare da rafka uban salati ta ce, “ikon Allah wato yan zun dan kin ganki da wannan ƙaton cikin wanda ba’a san uban sa ba shine kike ganin kin girma baki da kunya har kike zagi na, to mutanen gidan nan kuna jin abunda wannan marar kunyar take faɗa mani magana har da zagi,

Yaya! Yaya!! Kuzo ku gani kuma kuji da kunnen ku dan malam baya a raye shine zaki zage ni? dan kada ace nayi mata ƙazafi “.

Duk kan nin su matan gidan suka haɗu gurin ɗaya harda Umma na, tunda Umma na ta fahimci cewar dani ake wannan dramar sai ta koma gefe bata ce damu komai ba.

Exit mobile version