Waiwaye: Ci gaba da amfani da tsoffin kuɗi da sakin Emefiele
Waiwaye: Ci gaba da amfani da tsoffin kuɗi da sakin Emefiele
Kamar kowacce rana irin wannan, mun tattaro muku labaran muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata
A cikin makon da ya gabata ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargaɗi masu ƙin karɓar tsofaffin takardun Naira a faɗin ƙasar.
Wannan na zuwa ne sakamakon fargabar da ake ciki cewa tsofaffin takardun kuɗi za su daina aiki nan da watan Disamba 2023.
Wata sanarwar da mai magana da yawun bankin CBN, Isah Abdulmunin ya fitar a ranar Laraba, ta ce bankin bai bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kuɗi ba daga wajen al’umma.
Bankin ya ce, “An kuma samu rahotannin damuwa da wasu jama’a ke nunawa kan halacci ko rashinsa na tsoffin takardun kuɗin Naira.
Ga cikakken labarin a nan
Emefiele ya koma gida bayan shafe kwana151 a tsare
Haka kuma a ranar Larabar cikin makon da ya gabata ne wata babbar kotun Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.
Emefiele ya shafe kwanaki 151 a hannun jami’an tsaron Najeriya bayan sun kama shi cikin watan Yuni jim kaɗan bayan dakatar da shi daga aiki.
Kotun ta bayar da belinsa ne, duk da rashin amincewar babban lauyan gwamnatin tarayya, da hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa EFCC suka yi.
Mai shari’a Olukayode Adeniyi ya bayar da umarnin a saki tsohon gwamnan babban bankin, duk da cewa ta umarce shi da ya miƙa dukkan takardun tafiye-tafiyen sa na ƙasashen waje.
Tinubu ya saka hannu kan ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na 2023
A makon da muke bankwana da shi din ne kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya saka hannu kan ƙwarya-ƙwaryan ƙasafin kuɗi na shekara ta 2023 wanda ya kai naira tiriliyan 2.176.
Shugaba Tinubu ya saka hannun ne a ranar Laraba a fadarsa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar, ta ambato Tinubu na cewa kasafin kuɗin zai karfafa tsarin tsaron Najeriya da kuma magance matsalar giɓin ababen more rayuwa da Najeriya ke fuskanta, da sauransu.
Karanta cikakken labarin a nan
Gwamnan Oyo ya yi wa ma’aikata ƙarin naira 25,000 a albashinsu
A farkon makon nan ne Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa ma’aikatan jihar da ‘yan fansho za su riƙa karɓar tallafin kuɗi na naira 25,000 da kuma N15,000 a kowane wata na tsawon wata shida har sai an cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi.
Ya kuma jaddada muhimmancin ma’aikata da al’ummar jihar wajen haɗa hannu da gwamnatin jihar domin bunƙasa tattalin arzikin jihar na tsawon lokaci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga ma’aikatan a gidan gwamnatin jihar da ke Agodi a Ibadan.
Kotun ɗaukaka ƙara ta ce Lalong ne ya lashe zaɓen sanata a Filato
A cikin makon da ya gabatan ne kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke cancantar jam’iyyar PDP da ɗan takararta na sanata a mazaɓar majalisar dattawa ta Filato ta kudu, Napoleon Bali bisa zargin su da ƙin bin umarnin kotu.
Sa’ilin da take karanta hukunci, mai shari’a Elfreda William-Dawodu ta bayyana ƙuri’un da aka kaɗa wa PDP zaɓen sanatan Filato ta kudu a matsayin wofi, sannan ta bayyana tsohon gwamnan jihar ta Filato, Simon Lalong a matsayin zaɓaɓɓen sanata daga yankin.
Lalong, wanda ya yi takarar sanata a ƙarƙashin jam’iyyar APC, shi ne ya zo na biyu kamar yadda hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana a lokacin zaɓen na watan Fabarairun 2023.