Na rasa kusan duk ƴan’uwana a rikicin Isra’ila da Gaza
Na rasa kusan duk ƴan'uwana a rikicin Isra'ila da Gaza
‘Na rasa kusan duk ƴan’uwana a rikicin Isra’ila da Gaza’
14 Nuwamba 2023
Hare-haren Isra’ila ta sama sun shafe iyalai masu yawa da ke kan titunan Gaza, inda Falsɗinawa da yawa ke rayuwa cikin gidaje ɗaya. Wasu Falasɗinawa guda uku a Birtaniya sun faɗa wa BBC cewa an kashe ƴan uwansu sama da 20 a hari ɗaya – kuma da yawa sun makale cikin ɓaraguzan gine-gine.
A wata ranar Juma’a da rana shekaru huɗu da suka gabata lokacin da Ahmed al-Naouq ya ɗauki wannan hoto tare da iyalansa. Sai dai a yanzu, ya sake tuna lokacin.
Tsaye karkashin itacen zaitun a gidan mahaifinsa, ƴan uwansa sun zo da ƴaƴansu domin cin abinci, yin wasa da kuma tattaunawa.
Bayan katse wasa da suke yi, yaran sun shirya cin abinci lokacin da Ahmed ya ɗaukesu hoto. Yanzu, yawancinsu sun mutu, in ji shi.
Sun mutu ne sakamakon wani hari ta sama da ya faɗa kan gidansu a ranar 22 ga watan Oktoba. A jimilla, mutum 21 aka kashe ciki har da mahaifinsa, da ƴan uwansa mata uku, da ƴan uwansa maza biyu da kuma yaransu 14.
Sama da Falasɗinawa 11,000 aka kashe a lugudan wuta da Isra’ila ke yi, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza da ke karkashin ikon Hamas. Hare-haren ta sama sun fara ne bayan harin 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai, wanda Isra’ila ta ce ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,200 da kuma yin garkuwa da sama da 200.
Isra’ila ta ce tana kai hare-hare Gaza ne domin kawo karshen Hamas wadda ta zarga da fakewa cikin fararen hula – kuma da ganin an rage yawan fararen hular da ake kashewa.
A hoton da Ahmed ya ɗauka, yara bakwai ne kaɗai cikin waɗanda aka kashe suka bayyana a hoton. Wasu ba sa nan ranar da aka ɗauki hoton, yayin da ba a haifi wasu kuma ba.
Kamar sauran Falasɗinawa, ƴan uwan Ahmed sun gina gidajensu kusa da na mahaifinsu.
Ƴar uwarsa Aya ta je can ne domin neman mafaka tare da ƴaƴanta bayan da hari ya ruguza mata gida. Sauran ƴan uwansa, Walaa da Alaa, su ma suna can da ƴaƴansu. Gidan na tsakiyar Gaza a garin Deir al-Balah, wani yanki da ba a taɓa kai masa hari ba kafin yanzu. Mazauna wurin sun ɗauka za su tsira.
“Na ɗauka cewa yanzu lokaci ne mai ban tsoro garesu amma komai zai wuce,” in ji Ahmed.
Ahmed ya koma Lomdon ne shekaru huɗu da suka wuce domin aiki da wata ƙungiyar bayar da agaji kuma tun lokacin bai zo gida ba. Lokaci na karshe da ya ga ƴaƴansa shi ne magana ta kiran waya na bidiyon.
“Dukkansu sun ce suna son zuwa bakin teku domin shakatawa, cin abinci, yin rawa da kuma jin daɗi,” in ji shi. Don haka, ya ɗauki ya shirya musu liyafar da suke so.
Yaran sun kira shi daga bakin tekun a ranar, suna rige-rigen yin magan da shi ta waya.
Yanzu, yawancinsu sun mutu kuma Ahmed ya shiga ruɗani lokacin da ya tuna suna da kuma shekarun kowannensu.
Ɗan kanwarsa mai suna Eslam shi ne babba daga cikin yaran kuma ya fi saninsa. Ahmed ya kasance matashi da kuma ke zaune a gida loakcin da aka haifi Eslam. Mahaifiyarsa ita ta kula da jaririn lokacin da ƴar uwarsa ta tafi aiki, don haka so tari Ahmed yana taimakawa wajen kula da shi.
Yayin da Eslam ya fara girma, ya ce yana son zama kamar kawunsa. Shi ne ke kan gaba wajen hazaka a ajinsu, Ahmed ya ce Eslam ya yi ta ƙoƙari musamman a ɓangaren Turanci don ganin shi ma ya tafi zuwa Birtaniya.
An kashe Eslam tare da ƴan uwansa mata – Dima ƴar shekara 10, Tela shekara tara, sai Nour ƴar shekara biyar da Nasma shekara biyu, da Raghad shekara 13 da kuma Bakr shekara 11. Sai Eslam da Sarah ke da shekara tara, Mohamed da Basema shekara takwas yayin da Abdullahi da Tamim kuma ke da shekara shida.
Bayan harin, Ahmed ya wallafa hotunan dukkan yaran a shafukan sada zumunta domin duniya ta san abin da ya faru da su. Cikinsu akwai Omar ɗan shekara uku. Yaron yana kwance da mahaifiyarsa Shimaa da kuma mahaifinsa Muhammed – ɗan uwan Ahmed – lokacin da bam ya faɗa musu.
Daga nan Ahmed ya samu kiran waya daga wata ƴar uwarsa da ta tsira: Omar na raye. An kashe Muhammed ɗan uwan Ahmed, sai dai Shimaa da yaronta sun samu tsira.
“Wannan shi ne lokacin farin cikina a rayuwa,” in ji Ahmed.
Mutum ɗaya da aka samu damar cirewa daga ɓaraguzan ginin da ransa shi ne Malak ƴar shekara 11. Sai dai ta samu munanan raunuka da kuma kuna a kusan rabin jikinta.
Lokacin da na haɗu da Ahmed, ya nuna min hoton Malak tana kwance a gadon asibiti – an rufe dukkan jikinta da bendeji. Da farko, na ɗauka ita namiji ce maimakon mace saboda gashin kanta ba shi da tsayi. Ina ganin wuta ce ta ƙone sauran, in ji Ahmed.
Mahaifin Malak ba ya nan lokacin da hari ya faɗa ma gidansu kuma yana raye. Sai dai an kashe matarsa da yaransa biyu. Lokacin da Ahmed ya tura masa sakon cewa wane hali yake ciki, ya mayar masa da cewa: “Gangar jiki, babu rai.”
Mako daya bayan harin bam ɗin, an katse hanyoyin sadarwa gaba-ɗaya a Gaza yayin da Isra’ila ke kai hare-hare babu kakkautawa, kuma Ahmed bai samu damar magana da kowa ba. Lokacin da aka mayar da hanyoyin sadarwa kwanaki biyu bayan nan, ya samu labarin cewa Malak ta mutu.
Ana ci gaba da samun ƙarancin magunguna kuma an fitar da yarinyar mai shekara 11 daga ɗakin kula da masu tsanani na asibitin tare da saka wani wanda rashin lafiyarsa ta fi tsanani. Tana cikin matukar raɗaɗi.
“Ina mutuwa sau ɗari a kowace rana,” mahaifinta ya faɗa wa Ahmed, yayin da yake kallon lokacin da babban ɗansa kuma na karshe cikin ƴaƴansa uku ya rasu.
Jim kaɗan kafin a katse hanyoyin sadarwa, Ahmed ya kuma samu labarin cewa hari ya faɗa wa gidan kawunsa. Ba ya tabbacin wanda aka kashe can. A ranar Talata, ya kuma ji cewa hari ya shafi gidajen wasu abokanansa na kusa Maisara da Laura.
An kashe mutane da dama – Laura ta samu tsira sai dai ba a ga Maisara ba wanda ake kyautata zaton cewa yana makale karkashin ɓaraguzai.
Gabaki-ɗaya, mun tattauna da mutane guda uku a Birtaniya waɗanda suka rasa ƴan uwansu sama da 20 a Gaza.
Darwish al-Manaama ya faɗa wa BBC cewa an kashe ƴan uwansa guda 44. Cikinsu akwai ƴar kanwarsa mai suna Salma da mijinta, ƴaƴansu huɗu da kuma wani jikansu guda ɗaya.
Darwish ya gano cewa iyalansa sun mutu ne cikin wani jerin mutane da aka aika masa ta dandalin WhatsApp.
Yara Sharif, wata kwararriya kan harkar gine-gine kuma Malamar jami’a a Birtaniya, ta aika min hotunan gidan ƴar uwarta wadda harin Isra’ila ya lalata mako guda da fara yaƙi.
“Gidan yana matukar kyau,” in ji Yara, “Babban gida ne wanda kuma ke da lambu a tsakiyarsa.”
Kamar iyalan Ahmed, yaran sun gina gidajensu kusa da na iyayensu.
Yara ta samu labari a shafin Facebook cewa an kashe ƴan uwanta 20 – ƴar uwarta da kawunta, wasu ƴan uwanta da yaransu goma, ƙari da wasu mambobin iyalansu guda shida.
An ciro gawawwakin wasunsu daga cikin ɓaraguzan gine-gine kuma sun bayyana a jerin sunayen waɗanda ma’aikatar lafiya ta fitar da cewa sun mutu.
Yara ta aiko mana da hoton jerin kowane suna da ja, a gefen dama an saka shekarunsu. Sama tana da shekara 16, Omar da Fahmy tagwaye ne ‘yan shekara 14, Abdulrahman 13, Fatima 10, Obaida bakwai, shekarun ‘yan uwan Aleman da Fatima duk sun kasance biyar, Youssef na da huɗu sai Sarah da Anas su kuma uku.
Yara tana da ‘yan uwanta guda biyu da suka rage. Sun nemi a sakaya sunansu, suna cikin damuwa da kuma jin wata jita-jitar cewa ana kai wa waɗanda ke magana da manema labarai hari.
’Yan uwan mata suna sassa daban-daban a Gaza kuma ba za su iya ji daga junansu ba don yin jana’iza. Kuma duk da haka, ɗan uwan Yara ya aika mata sakon cewa: “Har yanzu Muhammad da Mama da kuma yaran biyu suna karkashin ɓaraguzai.”
Babu isasshen man fetur ɗin tafiyar da motocin haka a Gaza da kuma waɗanda ke aiki don ceto mutanen da ke raye.
A ranar Juma’a, yayin da na zauna tare da Ahmed al-Naouq muna kallon labarai, an nuna jerin sunayen waɗanda suka mutu. Na tambaye shi ko akwai ƴan uwansa a ciki. “Su 12 ne kaɗai,” in ji shi. Ba a gane sauran mutum tara ba zuwa yanzu.
Bayan lugudan bama-bamai, babbar ƴar uwarsa, wadda ke cikin gidanta lokacin da al’amarin ya faru, ta je domin wurin. Sai dai ta faɗa wa Ahmed cewa ta ƙasa tsayawa lokaci mai tsawo saboda ba za ta iya ci gaba da jin warin gawawwaki ba.
Ahmed ya sha wahala ji daga ƴan uwansa mata da suka tsira. Layukan waya ba sa tafiya akodayaushe, don haka ya daina ji daga garesu.
Yana ta faman neman kalmomin da turanci domin ya kwatanta abin da yake ji tun tashin bam ɗin, yana mai cewa kamar yanzu zuciyarsa ba ta cikin kirjinsa. Kuka ba shi ne abin yi ba, in ji shi, don ba zai canza kome ba.
“Ina jin kamar ba zan iya tsayawa ba, ba zan iya zama ba, ba zan iya yin barci da dare ba,” in ji shi. “Babu abin da za ku iya yi don dakatar da abin da kuke ji.”
Ahmed yace mahaifinsa shi ne mutumin kirki da ya taɓa sani. Ya yi aiki tuƙuru wajen tuƙin tasi da aikin gine-gine don gina wa ’ya’yansa gida da ba su ilimi da tarbiyya mai kyau.
Ya saurari labarai daban-daban kuma ya yi imanin cewa mafita ɗaya tilo da za a magance wannan rikici ita ce warware rikicin kasa ɗaya, inda Yahudawa da Falasɗinawa za su zauna tare da juna cikin lumana.
Amma yana tunanin ɗan uwansa ɗaya tilo da ya tsira, Ahmed yana mamaki: bayan wannan yaƙin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa da yake so, me Omar zai yarda?