Bayani kan maƙala
- Marubuci,Yogita Limaye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC News, Jerusalem
- 16 Nuwamba 2023
“Ɗiyata ba ta da suna har yanzu saboda yaƙin da ake yi. Kwananta huɗu,” in ji Keifaia Abu Asser. Zaune kan tabarma a cikin wata makaranta da suke zaman mafaka wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ke kula da shi a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.
Keifaia tana zaune riƙe da yarta, wadda ta rufe da jan bargo.
Ba abun da kake iya gani a fuskarta face gajiya da rashin samun barci. Zama uwa a karon farko a duniya yana da matukar wahala, sai dai yanayin ya zo wa Keifaia da tarin wahalhalu.
Ƴar asalin arewacin Gaza, matar mai shekara 24 ta tserewa gidanta ne tare da iyalanta bayan gargaɗin da sojojin Isra’ila suka yi wa fararen hula cewa su fice zuwa kudancin zirin Gaza domin tsira da rayukansu.
A lokacin Keifaia tana ɗauke da ciki, ta kuma kusa haihuwa.
“Dole ne na yi ta gudu daga wannan wuri zuwa wancan. Na gaji sosai. Da farko mun je sansanin Nuseirat. Sai dai an samu fashewar bam a kusa da mu. Na ga gawawwaki a warwatse, abu ne mai matukar wahala.” kamar yadda ta shaida wa wakilin BBC a Gaza.
Keifaia da iyalanta suna cikin dubun-dubatar mutanen da suka tsere daga arewacin Gaza kuma, kamar sauran mutane, ta yi tafiya mai nisan kilomitoci, duk cikin damuwar tashim bam.
“Yana da matukar haɗari ga yaron da ke cikina. Na kasance cikin tsoro akoyaushe,” in ji ta.
A karshe sun isa Asibitin Kuwaiti da ke birnin Rafah amma an rufe sashen kula da masu ciki. Daga nan aka kai Keifaa asibitin Emirati da ke kusa.
“Abin ya yi wahala sosai saboda yawan matan da suke haihu suna da yawa,” in ji ta. “Sun fito ne daga dukkan sassan Gaza, daga arewa zuwa kudu da kuma ko’ina a tsakanin.”
Ta kara da cewa “Akwai ƙarancin alluran rage raɗaɗi.” “Don haka suna gudanar da aikin kawai idan ciwon ya zama wanda ba za a iya jurewa ba kuma ga waɗanda suka fi buƙata.”
Ta haihu babu ba tare da yi mata alluran kashe raɗaɗi ba.
MDD ta ce tsarin kiwon lafiyar Gaza ya kusa durkushewa, kuma an rufe kusan kashi uku na asibitoci, abin da ya ƙara matsi ga asibitocin da ke aiki.
Ta yi kiyasin cewa kusan mata masu juna biyu 50,000 ne yaƙin ya shafa, kuma duk da irin yanayin da asibitocin ke ciki, ana sa ran samun mata da za su haihu 160 a kowace rana.
Mata masu juna biyu da dama ba sa samun kulawa yayin haihuwa, inda asibitoci suka cika da mutanen da suka jikkata a yaƙi, da ƙarancin man fetur domin tayar da injunan ba da hasken wuta, da rashin magunguna da kayayyakin buƙatu na yau da kullum – ciki har da matan da ke buƙatar kulawar gaggawa.
Ola Abu Oali na ɗaya daga cikinsu.
“Ƴarona yana da tsawon mako biyu a duniya. An haife shi ne lokacin yaƙi, a wannan makaranta da muke ciki,” kamar yadda ta faɗa wa Majdi Fathi, wakilin BBC da ke aiki a Gaza.
Ola tana kuma da wani yaro. Dukkansu suna cikin wani sansani da ya cika da mutane na MDD a birnin Rafah.
“Dukkan ƴaƴana ba su da lafiya. Suna fama da amai da gudawa, da ɗaurewar ciki. Duk lokacin da na bai wa yarona nono, sai ya yi amai. Sau uku ina kai ɗayan yarona asibiti domin samun kulawa, sai dai yanayin jikinsa bai canza ba,” in ji ta.
Samun tsaftataccen ruwan sha shi ne ɗaya daga cikin babban kalubale ga mutanen da yaƙi ya ɗaiɗaita a Gaza. MDD ta ce kowane mutum na da lita uku na ruwa ne kaɗai a rana wajen biyan buƙata.
“Ba mu da ruwan sha. Babu ruwan nonon da zan bai wa yarona. Kuma yanayin wuraren bahaya ba shi da kyaun gani. Akwai wari mara kyau da ke fita daga wajen kuma sai mun jira wasu sun gama abin da za su yi kafin mu yi amfani da shi,” a cewar Ola.
Wafaa Yousef Fakhry Ahmed na gudun hijira a cikin makarantar da Ola take zaune.
“Ina ɗauke da ciki. Ina tsoron abin da zai samu lafiyar yarona. Na kusa haihuwa kuma ina cikin damuwa kan muhallin da muke rayuwa a ciki, a kan kamuwa da cutuka. Ba mu da ruwan da za mu yi amfani da shi,” in ji Wafaa.
Ta ce ta fito ne daga birnin Beit Hanoun, kusa da iyaka da arewacin Gaza, kuma ta yi ta tafiya daga wannan wuri zuwa wancan domin samun tsira.
“Da farko, mun je wurin wata makaranta a yankin Al-Muaskar. An ce mana mu bar can ɗin ma, don haka muka tafi zuwa kudanci. Mun yi amfani da amalanke a wasu wurare kan hanyarmu ta tafiya. Sai dai sayyada muka taka yawanci a cikin tafiyar da muka yi,” in ji ta. “Ba mu da ruwan da za mu sha, don haka zaɓin da ya rage mana shi ne shan ruwa daga kogi. Mijina na ƙoƙari wajen samo mana roba ɗaya na ruwa domin mu sha.”
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana sa ran mutuwar mata masu juna biyu za ta ƙaru a Gaza sakamakon rashin samun isasshen kulawa.
WHO ta ce tashin hankalin yana da illa ga masu juna biyu, tare da samun ƙaruwar ɓarin ciki sakamakon damuwa, da haihuwar bakwaini.
Asma ‘yar birnin Gaza ce amma yanzu tana zaune da ‘ya’yanta uku a cikin wani sansani a harabar asibitin Al Aqsa da ke birnin Deir Al-Balah a tsakiyar Gaza.
Tana ɗauke da ciki kuma kafin a tilasta mata tserewa gidanta, ta je asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza domin a duba lafiyarta.
“Saboda ƙarar tashin bama-bamai, mata da yawa sun yi fama da ɓarin ciki a Al-Shifa, ba za a iya jurewa lamarin ba, musamman ga mata masu juna biyu. Na damu matuka game da jaririna da kuma ɓari.”
“Tashi da ciwo a sassan jikina ya zama abin da ke faruwa a kullum. Muna fuskantar rashin tsafta. Kuma mun sha ganin sassan gawawwaki da suka lalace,” in ji Asma.
Asma ta ce ta gaji matuka, kuma tana so a daina faɗa.
“Na roki a tsagaita wuta, mene ne laifin yara da za a saka su cikin wannan wahala? Mene ne laifin jaririna da nake ɗauke da shi?”