A ranar 17/1/2017 jirgin saman sojojin nigeria ya jefa bam a sansanin yan gudun hijira dake kauye a karamar hukumar mulkin (Kala Balge) a jahar Borno. Wanda yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 200 tare da raunana sama da mutum 90.
A ranar 5/9/2021 sojojin saman nigeria sun jefa bam akan yan uwa musulmi a kauyen (Buhari) a karamar hukumar mulkin yanusari dake jahar yobe. Wannan harin yayi sanadiyyar mutuwar yan uwa musulmi sama da 20 tare da raunana sama da mutum 40.
A watan April na shekarar 2020 jirgin saman sojojin nigeria ya hallaka mutum 17 mata da kananan yara a kauyen Sakotoku a karamar hukumar mulkin (Damboa) dake jahar Borno.
Bayan sati biyu da faruwar wannan, jirgin saman sojojin nigeria ya sake hallaka masu sana’ar kamun kifi mutum 20 a kauyen Kwatar Daban Masara dake tafkin chadi.
Jirgin saman sojoji ya hallaka wata mata da yayan ta 4 a kauyen Sububu dake jahar Zamfara.
Jiya 4/12/2023 jirgin saman sojoji ya jefo bam kan yan uwa musulmi a jahar kaduna, wanda yayi sanadiyyar hallaka sama da mutum 126 🥲🥲
Ni Alhassan Mai Lafia tambayar da nikeson nayiwa gwamnatin nigeria da rundunar sojojin saman nigeria shine:
- Meyasa duk wannan abun yake faruwa a arewa kadai??
- Meyasa duk wannan akan yan uwa musulmi yake faruwa??
- Shin rashin kwarewar aiki ne, ko ganganci ne?? Ko ana yakar arewa da musulmi ne a fakaice??
- Sannan shin wane mataki aka dauka domin magance wannan matsalar tun cen baya?? Wane irin bincike akayi domin sanin gaskiyar me ke jawo faruwar wannan??
- Shin an biya diyyar rayukan wanda iftila’in ya shafa??
- Meyasa ba’a hukunta sojojin saman dake wasa da rayuwar al’umma fafaren hula??
- Sakarkarun shugabannin mu na arewa, kucigaba da kallo ana karkashe mu. Mungode.
Alhassan Mai Lafia