Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu
Wanda aka sabunta Sa’a 1 da ta wuce
Kafofin yaɗa labarai a Najeriya na ba da rahotannin cewa, Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ce gwamnan ya rasu ne a ƙasar Jamus.
Ya rasu yana da shekara 67, bayan ya shafe lokaci yana fama da cutar kansar jini da ta mafitsara.
Rasuwar tasa na zuwa ne kimanin mako biyu, bayan ya rubuta wasikar tafiya jinya, inda ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.
Kafin sannan, an yi ta dambarwar siyasa a jihar Ondo, a kan yunƙurin tsige mataimakin gwamnan daga kujerarsa, amma daga bisani Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani.
Gwamnan dai ya shafe kusan wata uku a ƙasar Jamus yana jinya, daga bisani ya koma Najeriya a watan Satumba.
Sama da wata biyu bayan komawar Rotimi Akeredolu daga tafiyar jinyarsa ta farko, ba a iya ganinsa a bainar jama’a ba.
A watan Yuni ma, gwamnan ya karɓi hutun jinya na kwana 21, inda ya tafi Jamus, sai dai a wancan lokacin ya gaza komawa gida a lokacin da hutun jinyar nasa ya ƙare.
Da ya koma Ondo daga bisani kuma, sai ya aika wa majalisar dokokin jihar wasiƙa, inda ya sake neman ƙarin hutun jinya a ranar 15 ga watan Yuli.
- Manyan ‘yan takara uku da ke fafatawa a zaɓen gwamnan Ondo8 Oktoba 2020
- Gwamnan Ondo ya bai wa makiyaya kwana bakwai su bar dazukan jihar18 Janairu 2021
- Ƴan bindiga sun kashe masu ibada da dama a wata coci a jihar Ondo5 Yuni 2022
Yayin da rashin lafiyarsa ya tsananta, Gwamna Akeredolu ya fuskanci matsin lamba daga jam’iyyun adawa da ‘yan fafutuka don ya yi murabus ko kuma ya miƙa iko ga mataimakinsa, kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
A watan Oktoba, majalisar dokokin jihar ta rubuta wa alƙalin alƙalan Ondo wasiƙa, inda ta sake neman ya kafa kwamitin da zai binciki Lucky Aiyedatiwa a kan zarge-zargen aikata ba daidai ba. Mataimakin gwamnan ya garzaya kotu inda ya fara ƙalubalantar ƙoƙarin raba shi da muƙaminsa.
An zaɓi Akeredolu a matsayin gwamnan jihar Ondo a wa’adi na biyu a shekara ta 2020.
Ɗan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, ya fara cin zaɓen gwamna a watan Nuwamban 2016.
An haifi Arakunrin Rotimi Odunayo Akeredolu ranar 21 ga watan Yulin 1956, kuma ya halarci makarantar Aquinas College Akure kafin ya tafi Jami’ar Obafemi Awolowo University da ke Ile Ife.
Ya riƙe muƙamin kwamishinan shari’a na jihar daga 1997 zuwa 1999.
A 1998 ya zama babban lauya mai lambar SAN a Najeriya, sanan ya riƙe shugabancin ƙungiyar lauyoyi ta ƙasar tsawon shekara biyu daga 2008.