Akarshe wani mutum yaje nemawa dan autansa aiki a abuja sai shugaban ma’aikatar da yaga dattijon sai yace baba wane ka tunani sai dattijon yace ai bansankaba yaro, sai shugaban ma’aikatar yace kaine baban wane na gari kaza unguwa kaza sai dattijon yace eh nine ko ka sanni neh? Sai shugaban wajen aikin yace a shekara ta kaza mahaifina ya RASU wajenka nazo neman TAIMAKO tareda MAHAIFIYATA don biyan kudin MAKARANTA ka tura wani yaje ya ciro mana kudin hardana machine da abinci, sai dattijon yace gaskiya na mance kasancewar kafin nayi retirement mutane mabanbanta na zowa wajena neman TAIMAKO nikuma bayarwa kawai nake BATAREDA saina haddace mutaneba sannan banmasan yawan mutanenda nawa kalar taimakonda ka fadiba sai yaron yace tunda ka biyaman Babu kudinda na kuma kashewa domin a shekarar nayi kokari a makarantar na samu scholarship na fita karatu na gama na dawo nayi aiki wajaje mabanbanta har gani a wannan kujera meke tafe dakai, sai dattijon yace autana nazo nemawa aiki dakyarma na samu haduwa dakai sai da nabi hanyoyi masu yawa…nasan kunsan KARASHEN
domin sayan data mai sauki
www.forfordata.com.ng
Adon haka masu hanu da shuni ku sani DUNIYA teburi ce mai juyawa abinda ka shuka shi kake girba ko bayan ranka
Ku taimaki wada suke zowa wajenku musamman bangaren karatu, abinci, da muhalli, domin an mayarda KADUNA bariki SOSAI gashi mutanen cikinta mafi yawanci marasa karfine, ya UBANGIJI karka jarabcemu da abinda yafi karfin IMANINMU da ARZIKINMU subhanallahإنتنسر الله ينسركم ويثبت أقدامكم….