AMFANIN ILIMI AIKI DASHI
Allah Ya hore muku karanta abunda muke yin postn kullum,abunda ya rage kawai shine Fa’idar karatun wadda shine; aiki da abinda Muka Fadakar ko Muka koyar.
Ilimi ba tare Da aiki dashiba babbar Masiface,domin abin zargine a wajen Allah Da Manzonsa da Muminai.
Allah Madaukakin Sarki Yana cewa : YAKU MUMINAI ME YASA KUKE FADIN ABINDA BAKWA AIKATAWA ?? TSANANIN FUSHIN ALLAH YA TABBATA GAREKU IDAN KUKA FADI ABIN DA BAKWA AIKATAWA”.
Abu Hurairata R.A Yana cewa: “kwatankwacin Ilimin da Ba’a Aiki dashi kamar Taska ce da mai Ita Baya Ciyarwa Saboda Allah.
Ya ku ‘Yan uwan Bn Adam Mu dage da Yin aiki da abunda muka koya,domin Sahabban Annabi S.a.w sun kasance idan suka koyi wani abu sai suyi ta rige-rigen aiki dashi da kuma kira zuwa gareshi.
Har Imamu Ahmad (R) yana cewa: “Ban taba rubuta wani hadisi ba face sai nayi aiki dashi,Har saida naci karo da wani Hadisin da yake cewa, “wata rana Annabi s.a.w yayi Kaho sai ya baiwa Abu Dhaibata dinare daya,NI DA NAYI QAHO SAI NA BAIWA MAI KAHON DINARE”.
Mu kiyaye,MUYI AMFANI DA ILIMIN MU Kada mu sabawa Fadin Ma’aiki S.a.w da yake cewa: ” Idan na umurceku da wani abu to ku aikatashi gwargwadon ikon ku,abinda na haneku da shi kuma ku nisance shi.
Mu kuma jiyewa kanmu tsoron Uqubar Ubangiji da tazo acikin fadin Allah ( FALYAHZARIL LAZINA YUKHALIFUWNA AN AMRIHI,AN TUSIBAHUM FITNATUN AW YUSIBAHUM AZAABUN ALIM ) Ma’ana: “Masu sabawa umurninsa su kiyayi kansu,kar fitina ta samesu ko azaba mai radadi ta samesu.
Misalin yadda Magabata na kwarai ke amfani da iliminsu shine kamar misalin yadda Ummuna Habiba (R.A) data ruwaito Hadisin Annabi s.a.w da yake cewa: “Wanda ya sallaci raka’a goma sha biyu a dare da yini Allah zai gina masa gida a Aljannah”. Sai ta ce: “BAN TABA BARI WADANNAN SALLOLIN SUN WUCENI BA TUN SA’ADDA NAJI ANNABI (S.A.W) YA FADI WANNAN MAGANA”.
Kada mu kasance muna neman ilimi ba tare da aiki dashi ba,SAI MUYI KAMA DA YAHUDAWA DA ALLAH YAYI FUSHI DASU,ko kuma MUBAR NEMAN ILIMIN MU YI AIKI DA JAHILCI; Sai muyi kama da Nasara (Kirista) batattu.
Ina Rokon Allah Ya Azurtamu Da Ilimi Mai Amfani Da Aiki Managarci.