Aiko rahoto dagaAbuja- Sa’o’i 9 da suka wuce
Tsadar rayuwa na ƙara zama wani babban ƙalabule ga marasa karfi a Najeriya.
Hakan ya sanya mutane da dama sun koma yin girki da itace da kuma gawayi sakamakon tsananin tsadar gas ɗin girki.
Ƴan ƙasar dai na ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da fuskantar tsadar farashin gas, abin da ke gagarar ƴan ƙasar.
Mutane yanzu sun koma sayen gas daidai aljihunsu saboda tsadar gas ɗin na girki.
TALLA
Amma galibi masu ƙaramin karfin ne suka fi amfani da gawayi wajen yin girki.
Sai dai yayin da aka koma amfani da gawayin, masana kiwon lafiya na bayyana illolin da hakan ke da shi ga lafiya muddin ba a yi amfani da shi yadda ya dace ba.
Sun kuma ce sare itatuwa zai iya haddasa sauyin yanayi da ɗumamarsa, abin da kuma ƙasashen duniya ke yaƙi da shi.
Cutukan da gawayi ke iya haifarwa
“Gawayi yana da illoli da yawa, an fi samun su ko haɗuwa da su idan ana girki wurin da yake killace ba tare da kofofi ko taga ba. Kamar ɗakin da ba shi da taga,” a cewar Dr Salihu Ibrahim Kwaifa, wani kwararren likita a Abuja, babban birnin Najeriya.
Ya ce duk hayakin da yake fita daga girki kuma aka shaƙe shi, zai iya tayar da ciwon Asthma ga masu cutar, kuma yana kawo ciwon tari da kuma cutar lumoniya ga yara.
- Ƙauyen da kowa ke fama da ciwon mantuwa21 Janairu 2024
- Fiye da rabin al’ummar duniya za su yi fama da teɓa nan da 203513 Janairu 2024
- Yadda za ku kare yaranku daga cutuka bayan komawa hutun makaranta11 Janairu 2024
Dr Ibrahim Kwaifa ya ce amfani da gawayi ba bisa ƙa’ida kan iya janyo ciwon zuciya ga mutum.
“Muddin ba a samu wajen da hayaki zai bi ya fita ba, to hakan yana da babbar ila.”
“Wanda ke da ciwon huhu, cutarsa za ta iya tashi,” in ji shi.
Likitan ya ce gawayi na da wasu sinadarai waɗanda idan suka yi yawa za su iya janyo cutar sankara.
Ya ce yawan shaƙar ƙurar da ke cikin gawayi suna iya haddasa ciwon asthma ko kuma ta’azzararta.
Yadda za a yi amfani da gawayi
Likitoci kan bayar da shawarwari kan yadda mutane ya kamata su kula da lafiyarsu.
Dr Ibrahim Kwaifa ya faɗi wasu shawarwarin da mutane za su bi su kare kansu idan suna amfani da gawayi:
- A samu wurin da iska za ta riƙa ficewa
- Idan ana girki a riƙa fita ana shan iska
- A guji zama wurin girki a kodayaushe da kuma shaƙar hayaki
- Za a iya amfani da takunkumi lokacin yin girki
- A riƙa barin kofa ko taga a buɗe idan ana girki
Me ya kamata gwamnatoci su yi
Rashin wadatar makamashin zamani ne ke haifar da ci gaba da rungumar tsoffin hanyoyin samun makamashi musamman na girki.
Sabbin matakan makamashin kan yi tasiri ga rage barazanar sauyin yanayi da kuma taimakawa ga inganta lafiyar al’umma.
Masana na ganin gwamnatoci a dukkan matakai su ɗauki matakin rage farashin gas ɗin girki domin sauƙaƙawa mutane da kuma rage mu su faɗawa cikin illoli na yin amfani da gawayi.
Masana muhalli sun yi gargaɗin cewa muddin ba a ɗauki mataki ba, jama’a za su ci gaba da sare bishiyoyi don yin girki, abin da zai ci gaba da haifar da illar sauyin yanayi da gurɓatar muhalli .
Muddin kuma ana son daƙile sare bishiyoyi, dole a samar da makamashi mafi sauki da mutum zai yi amfani da shi.