content="218a3834dd422f26d2be19ac5e7d243b"/> Yadda ake amfani da sojojin haya na Amurka wurin kashe-kashe a Yemen - Samaniya Report News
LABARAN DUNIYA

Yadda ake amfani da sojojin haya na Amurka wurin kashe-kashe a Yemen

Huda al-Sarari

A yayin wannan bincike wakiliyar BBC ta kuma zanta da wasu gwamman majiyoyi a ƙasar Yemen waɗanda suka ƙara jaddada faruwar hakan. Ciki har da wasu mutane biyu waɗanda suka ce sun kashe wasu mutane da ba su da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci, bayan sun samu horo daga sojojin UAE. Sannan da wani mutum wanda ya ce an sako shi daga kurkukun UAE a madadin ya kashe wani babban ɗan siyasa a Yemen, tayin da ya ce bai amince ba. Neman mutanen Yemen su aikata kisan na nufin zai yi wuya a alaƙanta kisan da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan. A shekarar 2017, UAE ta taimaka wajen kafa wata rundunar tsaro, wadda ɓangare ce ta ƙungiyar (STC), da ke samun kuɗaɗe daga UAE, rundunar da ke aiki da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a fadin kudancin Yemen. Rundunar tana zaman kanta kuma ba ta ɗaukar umarni daga kowa sai daga UAE. Ba kawai an horar da mayanƙanta a fagen yaƙi ba ne, tana da wani sashe na, the elite Counter Terrorism Unit, wanda aka horar da su don aikata kisan kai, mai kwarmaton ya shaida wa BBC. Mai kwarmaton ya aiko da wata takarda mai ɗauke da sunayen tsoffin mayaƙan al-Qaeda 11, kuma a yanzu suna aiki da STC, BBC ta tabbatar da wasu daga cikinsu. Haka kuma a yayin wannan bincike, an yi karo da sunan Nasser al-Shiba. Wani wanda ya taɓa zama babban ƙusa a al-Qaeda, an ɗaure shi kan ta’addanci, amma daga bisani aka sake shi. Wani minista a gwamnatin Yemen wanda ya shaida wa BBC cewa al-Shiba sanannen wanda ake zargi ne da kai hari kan jirgin ƴakin Amurka USS Cole, lamarin da ya kai ga mutuwar sojojin ruwan Amurka 17 a watan Oktobar 2000. Majiyoyi da dama sun gaya wa BBC cewa a yanzu shi ne kwamandan wasu sassan sojin ƙungiyar ta STC. Lauya Huda al-Sarari tana bincike kan keta haƙƙin bil-Adama da sojojin da ke samun goyon bayan UAE suka aikata a Yemen. Ta sha samun barazanar kisa saboda aikinta, amma ɗanta mai shekara 18 ne ya rasa ransa a kan hakan. An harbe shi a ƙirji a watan Maris 2019 a lokacin yana kan hanyar zuwa wani gidan mai, kuma ya mutu wata guda bayan hakan ta faru. Lokacin da Huda ta koma bakin aiki ta ce ta samu saƙonnin da ke gargaɗinta da ta daina. “Ɗa guda ɗaya bai ishe ki ba, kina son mu kashe sauran?” Suka ce mata. Wani binciken da mai gabatar da ƙara na Aden ya yi daga baya, ya gano cewa wani ɗan ƙungiyar da ke samun goyon bayan UAE ne ya kashe Mohsen, sai dai ba a taɓa kama kowa da laifi ba. Wasu jami’an ofishin ma su gabatar da ƙara – waɗanda ba za su iya ambata ba sun shaida muna cewa yawaitar kashe-kashen sun samar da wani yanani na ban-tsoro wanda ya kai su kansu suna tsoron gabatar da ƙara kan laifukan da suka shafi dakarun da ke samun goyon bayan UAE. Mun tambayi wanda ya samar da Spear, Abraham Golan, kan ko sojojin hayarsa ya horar da ƴan UAE dubarun kisa, amma bai ce komi ba. Mun taƙaita zarge-zargenmu ga gwamnatin Daular Larabawa. Ta ce ba gaskiya ba ne cewa tana kama waɗanda ba su da alaƙa da ta’addanci. Kuma tana goyon bayan goyon baya ga gwamnatin Yemen. “UAE ta kiyaye dokokin kasa da kasa a lokacin ayyukanta,” a cewarta. Mun tambayi ma’aikatar tsaron Amurka da ma’aikatar harakokin waje su yi magana game da ayyukan Spear amma ba su ce komi ba. Hukumar leƙen asirin Amurka a cikin wata sanarwa ta ce: Batun cewa CIA na da hannu ba gaskiya ba ne.”

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button