Gwamnatin Tarayya, A ƙarƙashin Jagorancin ma’aikatar masana’antu, Kasuwanci da zuba jari ta Tarayya (FMITI), ta samar da Wasu kuɗaɗe Guda uku da suka kai Naira Biliyan 200 Domin Tallafawa wa ‘yan kasuwa a faɗin ƙasar.

Gwamnatin Tarayya, A ƙarƙashin Jagorancin ma’aikatar masana’antu, Kasuwanci da zuba jari ta Tarayya (FMITI), ta samar da Wasu kuɗaɗe Guda uku da suka kai Naira Biliyan 200 Domin Tallafawa wa ‘yan kasuwa a faɗin ƙasar.

Bankin masana’antu (BOI) ne zai fitar da waɗannan kuɗaɗen kuma zasu ɗauki kuɗin Ruwa na kashi tara cikin dari.

Hakazalika, haɗin Gwiwar da Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC) tayi a jiya da Bankin Moniepoint Micro Finance, ya haifar da yin rajistar Wasu fitattun masana’antun, ƙanana da matsakaitan sana’o’i (MSMEs) Miliyan biyu, Tare da halatta ayyukansu a cikin kasa.

Gwamnatin Tarayya ta samar da wasu kuɗaɗe Domin Tallafawa wasu tsare-tsare da suka haɗa da shirin bayar da tallafin sharadi na Shugaban kasa (PCGS), asusun saka hannun jari na FGN MSME, da asusun samar da kayayyaki na FGN. An bada alhakin Gudanar da ayyukan yau da kullun na Wadannan kudade ga bankin masana’antu (BOI), wanda aka nada a matsayin hukumar zartarwa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Dokta Olasupo Olusi, Manajan Darakta/Babban Jami’in Gudanarwa na BOI, ya jaddada sadaukarwar BOI ga ci gaban MSMEs, tare da sanin muhimmiyar rawar da suke takawa a cikin tattalin arziki

Olusi yace, “Tsarin bayar da tallafin sharadi na Shugaban kasa (PCGS) shiri ne na tallafin Naira biliyan 50 don tallafa wa masu kananan sana’o’i Za’a bayar da tallafin ne ga mafi ƙarancin Mutane 1,000 da Zasuci Gajiyar Tallafin, Musamman mata da matasa a kowace ƙaramar Hukuma (LGA) a ƙananan Hukumomi 774 dake faɗin ƙasar nan da kuma ƙananan Hukumomi shida na Babban birnin tarayya Abuja.

“Kasuwancin da ake shirin inganta wa sun haɗa da ‘yan kasuwa, masu siyar da abinci, kasuwancin ICT, masu sufuri, masu sana’a, da masu ƙirƙira, da sauransu.

Dole ne mutum ya kasance ya cike Waɗannan sharuddan Kafin yasamu Tallafin karamar hukuma da Kuma sana’ar da kake Sannan kuma bayanan asusun banki, Lambar BVN) da Lambar Shaida ta Zama ɗan Kasa (NIN) don tantancewa.

Exit mobile version