FOOTBALL
MENE NE AZUMI
MENE NE AZUMI…?
- AZUMI A LUGGA
Shine kamewa - ASHARI’ANCE:- Shine kamewa daga barin chi ko sha da saduwa da iyali tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada.
RUKUNAN AZUMI
- Yin niyya
- Kamewa dagachi ko sha da saduwa da iyali
- Zamani (lokachin yin azumi).
SUNNONIN AZUMI
- Gaggauta buda baki
- Jinkirta sahur
- Addu’a yayin buda baki
- Yin sahur da jinkirta shi.
MAKARUHAN AZUMI
- Kaiwa matuka wajen kurkuran baki
- Sumba
- Dauwamar da kallo na sha’ awa
- Tunani akan al’amuran saduwa
- Shafa ko runguma
- Dandanan wani abu
- Sanya tozali
- Yin kaho.
ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI
- Saduwan wani abu zuwa makoshi (narkakke)
- Fitarda maniyyi ko maziyyi da gangar
- Saduwa ta hanyar tilasta
- Chi ko sha da tunanin sauran dare
- Chi ko sha da gangan
- Saduwan wani abu wanda ba narkakkeba zuwa makoshi
- Ridda.
ABUBUWAN DA SUKE HALAS
- Yin asiwaki
- Sanyaya jiki da ruwa
- Tafiya ta halas
- Sanya magani wanda ya dache
- Tauna wani abu ga karamin yaro
- Sanya turare.
ABUBUWAN DA AKAYI RANGWAME
- Hadiye yawu
- Rinjayen amai da magwas
- Rinjayen wani kwaro zuwa ga makoshi
- Kuran kan hanya
- Wayan gari da janaba
- Yin mafarki da rana
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.