Menene Bitcoin Halving
Menene Bitcoin Halving: A yau za'a kafa sabon tarihi za ayi BTC halving na hudu daga cikin halving guda 20 da za'a yi akan Bitcoin da Blockchain dinsa, wanda aka tsara za'a yi a cikin shekaru 128, an fara Bitcoin halving a 2012 za'a kammala a 2140 shekaru 116 masu zuwa, a lokacin zai cika halving guda 20 cif.
Menene Bitcoin Halving:
A yau za’a kafa sabon tarihi za ayi BTC halving na hudu daga cikin halving guda 20 da za’a yi akan Bitcoin da Blockchain dinsa, wanda aka tsara za’a yi a cikin shekaru 128, an fara Bitcoin halving a 2012 za’a kammala a 2140 shekaru 116 masu zuwa, a lokacin zai cika halving guda 20 cif.
Da misalin karfe 1:34am na daren da muke ciki (in sha Allah) za’a yi Bitcoin halving na hudu daga cikin jerin halving guda 20 da za’a yiwa Bitcoin (4/20), halving din zai zo akan Block height na dubu 840,000. Ana yin Bitcoin halving ne duk bayan shekaru 4, a duk lokacin da aka yi adding Blocks of transactions guda dubu dari 210,000 akan Bitcoin Blockchain.
~ Miners suna iya yin Mining Block guda daya a duk bayan Mintoci 10, hakan yana nuna sai an shafe shekaru 4 kafin a shigar blocks guda dubu dari 210,000.
Bitcoin Halving:
Asali, tunda farko Satoshi Nakamoto yayi Bitcoin da adadin da suka kai guda Miliyan 21,000,000 dai dai. Amma ba’a iya samun sabbin Bitcoins sai idan Miners sun hako su ta hanyar hakan Bitcoin, wato (Bitcoin Mining), idan sun hako ne ake samun sabbin Bitcoins da zasu shiga kasuwa, dan haka har yanzu ba’a gama hako Bitcoin gaba daya ba.
~ Daga 2009 zuwa yanzu 2024 an hako Bitcoin guda Miliyan 19 da dubu dari 680,000 wato (19,680,000) sune Bitcoin din da suke circulating suke kasuwa, suke hannun mutane, sune ake iya saya ko siyar dasu.
Hakan yana nuna akwai sauran Bitcoin, ragowar Bitcoin guda Miliyan 1 da dubu 320,000 (1,320,000) da za’a kammala hako su nan da shekaru 116 masu zuwa, wato a dai dai shekarar 2140.
Menene Bitcoin Halving:
Bitcoin halving yana nufin raguwar abinda Bitcoin miners suke samu da kaso Hamsin.
An fara Bitcoin halving a 2012, kafin 2012 wato tsakanin 2009 da 2010 Miners suna samun Bitcoin guda 50 a duk lokacin da suka yi Mining block guda daya.
~ Anyi Bitcoin halving na farko a ranar 28 November 2012, daga lokacin Miners suka koma samun Bitcoin guda 25 maimakon 50.
~ BTC halving na biyu anyi shi ranar 9 July 2016, Miners suka koma samun 12.5
~ Ranar 11 May 2020 aka yi Bitcoin halving na uku, Miners suka koma samun 6.25.
Kuma abinda suke samu kenan yanzu haka.
Da misalin karfe 1:44 na daren nan da muke ciki na ranar (20 April 2024) za’a yi Bitcoin halving na hudu, Miners zasu koma samun Bitcoin guda 3.12 BTC.
~ Za ayi halving na biyar ranar 14 April 2028, Miners zasu koma samun 1.56 BTC.
Daga nan sai Halving na 6, zasu fara samun ‘kasa da Bitcoin daya, wato 0.78 BTC.
Za’a kammala Bitcoin halving ne a shekarar 2140, wato shekaru 116 masu zuwa, idan Allah ya bar duniyar ta kai lokacin.
Idan mun fahimci wannan zamu gane cewa sabbin Bitcoin da suke shigowa hannun mutane wato new circulating coins da ake samun guda 6.25 zai koma 3.125 BTC.
~ Base on the principals of Demand and supply idan supply na Bitcoin ya ragu kuma demand ya karu toh dole farashi zai tashi, wannan haka yake a kowace irin kasuwa ba kadai Bitcoin ba.
Bull Run (lokacin samun riba a kasuwar Crypto) yakan zo mostly duk bayan shekaru hudu bayan anyi Bitcoin halving da watanni.
A yanzu za’a ga tashin Bitcoin da sauran crypto assets irin wanda ba’a taba gani ba a tarihi, saboda wasu manyan abubuwa guda biyar:
- Bitcoin halving.
- Bitcoin Spot ETF Approved.
- Bitcoin Open adoption.
- New technologies, kamar scaling solutions da aka yi wa Ethereum (wato layer two, L2) da wadanda aka yiwa Bitcoin (BTC L1 da L2).
- Bitcoin Non custodial Staking, powered by CORE Foundation.
So, a cikin wannan daren za’a kafa tarihi me girman gaske.
Sai dai Bitcoin halving ba wasu mutane bane suke yi, ko wasu Masana, No, ba haka abun yake ba, system din ne yake yi duk bayan shekaru hudu, Blockchain din BTC da yake amfani da PoW (Proof of Work) yake yi, so duk duniya babu wani mutum da yake da hannu akan BTC halving. Kowa zuba Ido yake yi yaga ikon Allah yadda abun yake gudana.
Amma yana da kyau mu fahimci ba da zaran anyi Bitcoin halving ne kasuwar Crypto take mikewa ba, ba haka abun yake ba, sometimes akan samu watanni ko ma shekara daya bayan anyi halving, misali anyi Bitcoin halving a watan May 2020, amma Bitcoin bai tashi zuwa New ATH ba sai bayan shekara daya daya da watanni 6, wato November 2021 a lokacin BTC yaje 69,000 Dollars.
Sai dai a wannan karon ana hasashen Bitcoin zai fara mikewa kwanaki kadan bayan halving ba wai watanni masu yawa ba, saboda Factors masu yawan gaske.
~ Amma da zaran anyi halving Bitcoin zai Fadi, zai sauka kasa sosai, dan haka sai a shirya, hakan zai faru ne saboda kasuwar zata sake daukan sabon direction, sai an fahimci directions din kafin kudade su fara flowing cikin Bitcoin da sauran tokens da NFTs.
Bangarori da zasu fi daukan hankalin duniya kuma ake ganin kudade zasu shiga cikin projects din, su sune:
- AI (Artificial Intelligence).
- Social Fi.
- RWA.
- DePIN.
- DeFi.
Da sauran su.
A 2011 Bitcoin yana $0.3, amma bayan anyi halving a 2012 Bitcoin yaje $12.
A 2015 Bitcoin yana Dala $362 bayan anyi halving a 2016 Bitcoin ya haura Dala dubu 6,200 a tsakanin 2017, 2018 da 2019.
A 2020 Bitcoin yana Dala dubu 6,200.
Bayan anyi halving sai da yaje Dala dubu 69,000 a Nov 2021.
A yanzu ba’a yi halving ba, amma Bitcoin yaje sama da Dala dubu 70,000 kafin ya dawo ya tsaya a Dala dubu 64,000 a yanzu.
Bitcoin shine kasuwar Crypto, idan ya tashi toh kusan komai zai yi daraja, kaso 80 na kasuwar, kamar Man Fetir ne, idan yayi tsada komai zai yi tsada, idan ya fadi komai zai yi sauki.
~ Bitcoin sai manyan masu Kudi, amma shine yake da 50 percent na crypto market dominance, akwai tsaban Kudi a cikin kasuwa crypto sama da Dala Trillion biyu a yanzu, amma sama da Dala trillion 1.2 suna cikin Bitcoin ne shi kadai.
Saboda karfin sa, security da Decentralization dinsa. Sauran coins guda dubu 25,000 da suke kasuwar Crypto sune suka dauki ragowar Dala Trillion daya a yanzu.
Wannan yana nuna maka irin yadda masu Kudi suka yarda da Bitcoin da tsaron dake kansa.