content="218a3834dd422f26d2be19ac5e7d243b"/> Me ya faru a hare-hare kan sansanin Falasɗinawa a Rafah? - Samaniya Report News
LABARAN DUNIYA

Me ya faru a hare-hare kan sansanin Falasɗinawa a Rafah?

Me ya faru a hare-hare kan sansanin Falasɗinawa a Rafah?

Yaro tsaye a kusa da konanniyar mota

Bayani kan maƙala

  • Marubuci,Ahmed Nour, Abdirahim Saeed and Shereen Sherif
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,samaniyareport News Arabic
  • 1 Yuni 2024

Akalla mutum 45 ne aka kashe a harin sama da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijrar Falaɗinawa da ke birnin Rafah da ke kudancin Gaza ranar 26 ga watan Mayun 2024, kamar yadda ma’aikatar lafiya da ƙungiyar Hamas ke iko da ita ta ce. Da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa mata ne da ƙananan yara.

Falasɗinawa da wasu ƙungiyoyin agaji sun ce wurin da aka hara ɗin wuri ne da aka tanada ya zama “amintacce” daga hare-hare.

Dakarun Isra’ila na IDF sun musanta hakan sannan sun ce sun hari maɓoyar wasu manyan shugabannin Hamas ne guda biyu da ke wajen ‘amintaccen” wurin fakewar ‘yan gudun hijra da aka kafa domin fararen hula.

Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana mutuwar fararen hula da “haɗari abin takaici” a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke ci gaba da yin allawadai dangane da harin.

An dai kai harin ne kan sansanin ‘yan gudun hijra inda wasu kafafen watsa labaran Falaɗinawa sun fara rawaito cewa al’amarin ya faru ne a “amintaccen wurin ‘yan gudun hijra” da rundunar IDF ta ayyana a baya.

Yadda sansani ya ci wuta

Sashen BBC na Larabci ya yi ƙoƙarin haɗa haƙiƙanin abubuwan da suka faru a yayin mummunan harin – inda suka duba bidiyo da hotuna da sauran shaidu da suka haɗa da waɗanda suka shaida yadda abin ya faru.

Wasu bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta dangane da harin na dakarun IDF a kan sansanin da ke arewa maso yammaci Rafa sun fara bayyana ne a intanet da misalin ƙarfe 10 lokacin ƙasar wato daidai da ƙarfe 7 agogon GMT, na ranar 26 ga watan Mayu.

Wasu hotunan farko-farko sun nuna yadda gagarumar wuta ta tashi a sansanin na wucin gadi, a lokacin da jiniya da kururuwar jama’a suka cika kunne.

Harwayau, waɗansu hotunan masu motsi da ke da tsoratarwa sun nuna yadda mutane ke zaro jikkunan da suka yi gunduwa-gunduwa da ma jikin wani yaro da kansa ya cire.

Hotunan da aka ɗauka na rana sun nuna cewa al’amarin ya faru ne a sansanin “Kuwaiti Salam na 1”.

Wasu bayanan da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun rawaito cewa sansanin ya kasance a arewaci kusa da cibiyar hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai ba wa Falaɗinawa agaji ta UNRWA da ke Tal al-Sultan da ke Rafah.

Nisan da ke tsakanin wuraren guda biyu kamar yadda hotunan tauraron ɗan’adam suka nuna bai wuce mita 200 ba.

Wurin da sansanin yake

A ranar 28 ga watan Mayy, dakarun IDF sun fitar da wata taswira da ke nuni da wurin da aka kai harin a matsayin daya daga cikin wuraren da BBC ta gano.

Hotunan tauraruwar ɗan adam daga ranar 27 ga watan Mayu sun nuna irin girman lalacewar abubuwa kan wurare guda biyar da yankin da abin ya shafa.

Dakarun rundunar IDF sun ce sun ƙaddamar da harin ne ta hanyar amfani da “makamai da suka nufi yadda ake so’ kuma sun kashe manyan jagororin ƙungiyar Hamas guda biyu. Sun kuma ce suna bincike na mutuwar fararen hula a yankin.

Isra’ila ta ce ta yi amanna cewa wutar da ta tashi a tantunan ‘yan gudun hijra ka iya zama sanadin manyan fashewar abubuwa a rumbun ajiyar makamai na Hamas da ke kusa. Sai BBC ba ta iya gano hakan ba.

‘Tundun mun tsira’?

An samu rashin amincewa dangane da matsayin wurin da sansanin yake.

Falasdinawa da da dama daga cikin ƙungiyoyin duniya masu agaji sun dage cewa wurin da aka kai harin “amintacce” ne daga kai hare-hare da sojojin Isra’ila suka ayyana. Sojojin dai sun musanta hakan.

“Amintaccen” na nufi da wuraren da rundunar IDF ta ayyana a matsayin tudun mun-tsira da ke kudancin Gaza.

Wuraren sun tankarar da arewacin bahar-aswad daga al-Mawasi – wani ɗan ziri da ke da albarkacin noma – daga birnin Khan Younis da kuma garin Deir al-Balah da ke tsakiya.

Rundunar IDF dai ta daɗe tana umartar fararen hula da su koma yankin tun watan Oktoban bara.

A farkon watan Mayu, rundunar ta umarci mutane a gabashin Rafah da su koma zuwa “yankin jinƙai” kafin fara kai hare-hare ta ƙasa.

A wani ɓangare na gargaɗin kwashe mutane zuwa tudun mun tsira, kamar yadda dakarun na IDF suka sha amfani da taswirar Gaza wanda a cikinsa aka karkasa garin zuwa gidajen da aka yi wa lambobi.

Wani mai magana da yawun rundunar ta IDF, a shafinsa na X, a ranar 22 ga watan Mayu, ya faɗi cewa wurin da ake keɓe da “yankin jinƙai an faɗaɗa shi zuwa yankunan da ke kudancin Khan Younis da ya haɗa da gidaje masu lamba 2360, 2371 da 2373.

Mun gano wurin da tantunan da harin na Isra’ila ya shafa kuma sun nuna cewa gida ne mai lamba 2372 wanda yake a wajen yankin jinƙai da rundunar IDF ta ayyana.

‘Umarnin da ba a fayyace ba’

Wasu Falasɗinawa da suka yi tattauna da kafafen watsa labarai, sun ce sun yi amanna cewa tantunan na yankin “tudun mun tsira ” da dakarun IDF suka ayyana.

“Ƴan mamaya (dakarun Isra’ila) sun shaida mana cewa wannan wurin yana da aminci kuma za mu iya tsayawa a wurin tunda amintacce ne, to amma babu wani wuri mai aminci a nan zirin Gaza,” In ji Jamal al-Attar, wani wanda ya shaida abin da ya faru.

“Sun kashe mana yara da ƙona matanmu da tsaffi a cikin wurin da ake kira wai amintaccen wuri,” ya ƙara faɗi.

Kimanin mutum miliyan ɗaya da rabi ne ke neman mafaka a Rafah tun kafin ranar 6 ga watan Mayu, lokacin da Isra’ila ta fara abin da kira da hare-haren ƙasa na “wuraren da aka nufa” a gabashin birnin.

Ƴan awanni dai kafin fara harin na Isra’ila, Hamas ta harba rokoki takwas daga Rafah zuwa Tel Aviv – irinsa na farko mai dogon zango a kan birnin na Isra’ila tun watan janairu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kiyasta cewa fiye da mutum 800,000 suka tsere bisa umarnin rundunar IDF cewa jama’a su yi kaura zuwa “tundun mun tsira”.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button