Real Madrid ta ɗauki Champions League na 15 jimilla
1 Yuni 2024
Real Madrid ta lashe Champions League na bana na 15 jimilla, bayan da ta doke Borussia Dortmund 2-0 ranar Asabar a Wembley.
Tun farko sun tashi ba ci a zagayen farko da suka koma zagaye na biyu ne Real ta ci ƙwallon farko ta hannun Daniel Carvajal da kuma Vinicius Junior.
Kenan Vinicius Junior yana da hannu a cin ƙwallo 22 a Champions League, wanda ya ci ƙwallo 11 ya kuma bayar da 11 aka zura a raga.
Kenan ya yi kan-kan-kan da Lionel Messi a yin wannan bajintar tun kafin ya cika shekara 24 da haihuwa.
Karon farko da Jadon Sancho da Jude Bellinhgam da suka fuskanci juna wato ƴan wasan tawagar Ingila a karawar ƙarshe a ko dai European Cup/UEFA Champions.
To sai dai Dortmund ta samu damarmaki da yawa na cin ƙwallo, inda dama biyu kaɗai Real ta samu a zagayen farko.
Wannan shi ne wasa na biyu da Real ta kasa taka rawar gani a zagayen farko a gasar ta zakarun Turai ta bana.
Wannan shi ne karo na 15 da suka fuskanci juna a tsakaninsu kuma a Champions League, inda Real ta yi nasara bakwai da canjaras biyar, Dortmund ta ci uku.
Karo na biyu da Dortmund ta yi rashin nasara a Wembley a wasan karshe a Champions League, bayan da Bayern Munich ta doke ta 2-1 a 2013.
Carlo Ancelotti ya lashe Champions League na biyar a matakinsa na kociya, sannan na uku a Real Madrid.
Ɗan kasar Italiya ya ɗauki biyu a AC Milan a 2002–03 da 2006–07, sannan ya lashe uku a Real Madrid 2013–14 da 2021–22 da kuma 2023–24.