Me zai faru idan Ukraine ta yi amfani da makamai masu dogon zango kan Rasha?

Me zai faru idan Ukraine ta yi amfani da makamai masu dogon zango kan Rasha?

Me zai faru idan Ukraine ta yi amfani da makamai masu dogon zango kan Rasha?

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky
Bayanan hoto,Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya shafe tsawon watanni yana neman a ba shi damar harba makamai masu linzami masu dogon zango kan Rasha

Sa’o’i 3 da suka wuce

Jami’ai a Amurka sun ce shugaba Joe Biden ya bai wa Ukraine damar amfani da makamai masu cin dongon zango da Washington ɗin ta ba ta, domin far wa Rasha.

A baya, Washington ta ki amincewa da amfani da makaman na ATACMS wadda ƙasar ta ƙera, saboda tana fargabar cewa hakan zai janyo munanan yaƙi.

Amincewa da amfani da makaman masu cin dogon zango na zuwa ne watanni biyu kafin shugaba Joe Biden ya miƙa ragamar mulki ga sabon zaɓaɓɓen shugaba Donald Trump, wadda nasararsa ta sanya shakku kan makomar taimakon da Amurka ke bai wa Kyiv.

Me ya sa Amurka ta ba Ukraine damar amfani da makamai masu dogon zango kan Rasha?

Ukraine ta ɗauki tsawon lokaci tana amfani da nau’in maƙamai waɗanda ake kira ATACMS, wajen kai hare-hare kan Rasha musamman a yankunan ƙasar da Rashar ta mamaye sama da shekara ɗaya.

Sai dai Amurka ba ta taɓa bai wa Kyiv damar amfani da makaman linzami masu dogon zango ba zuwa cikin Rasha – sai yanzu.

Makaman masu linzami sune mafiya ƙarfi da aka bai wa Ukraine kawo yanzu, waɗanda za su iya tafiyar kilomita 300 a sama.

Ukraine ta ƙalubalanci cewa hana ta amfani da irin waɗannan makamai a yaƙin da take yi da Rasha kamar tilasta mata yin faɗa da hannu ɗaya ne.

An ruwaito cewa matakin na zuwa ne a matsayin martani na tura dakarun Koriya Ta Arewa domin zuwa su taimaka wa Rasha a iyakar yankin Kursk, wanda Ukraine ta mamaye tun a cikin watan Agusta.

Haka kuma, komawa fadar White House da Donald Trump ya yi, ta sanya fargaba kan makomar taimakon da Amurka ke bai wa Ukraine, kuma shugaba Joe Biden na iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya taimaka a ɗan ƙankanin lokaci da ya rage masa kan mulki.

Ƙara wa Ukraine ƙarfin soji – zai ba ta damar ta yi yadda take so a duk wata tattaunawar zaman lafiya a nan gaba.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky bai kai ga tabbatar da matakin ba.

Yaƙin Ukraine
Bayanan hoto,Nan maƙaman linzami ne masu dogon zango da aka harba waɗanda za su iya tafiyar kilomita 300 a sama, lokacin wani atisayen sojojin Koriya Ta Kudu

Wane tasiri makaman za su yi a fagen daga?

Ukraine za ta iya kai farmaki cikin Rasha a yanzu, musamman ma farawa ta yankin Kursk, inda dakarun Ukraine ɗin ke riƙe da wani babban yanki.

Ƴan Ukraine da kuma jami’an Amurka na sa ran martani daga Rasha da kuma dakarun Koriya Ta Arewa domin sake ƙwace iko da yankin Kursk.

Ukraine za ta iya amfani da makaman na ATACMS domin kare kanta, inda za ta hari muhimman wurare a Rasha, ciki har da sansanin sojoji, gine-gine da kuma wurin ajiyar makamai.

Samar da makaman linzamin ba zai sa akalar yaƙin ya sauya ba.

Tuni aka aika makaman sojin Rasha kamar jiragen yaƙi masu saukar ungulu zuwa filin saukar jirage can cikin Rasha domin shirin ko-ta-kwana.

Sai dai makaman za su iya bai wa Ukraine wata dama a daidai lokacin da sojojin Rasha ke ƙara ƙwace wurare a gabashin ƙasar.

“Ba na tsammanin matakin zai kawo wani sauyi,” kamar yadda wani masanin diflomasiyyar ƙasashen Yamma ya faɗa wa BBC, inda ya nemi a sakaya sunansa saboda girman batun.

“Duk da haka, mataki ne da zai ƙara musu karsashi da kuma nuna taimakon soji ga Ukraine.

“Ɗawainiyar da Rasha take yi ko kudin da take kashewa a yaƙin zai ƙaru a yanzu.”

Akwai kuma tambaya kan yawan harsasai da za a samar, a cewar Evelyn Farkas, wadda ta taɓa zama mataimakiyar sakataren tsaro a lokacin mulkin Obama.

“Tambayar ita ce, makamai masu linzami nawa suke da shi? Mun ji cewa Pentagon ta yi gargaɗin cewa babu makamai masu linzami da yawa da za su iya samar wa Ukraine.”

Farkas ta ƙara da cewa makaman na ATACMS “za su yi tasiri sosai a yaƙin Ukraine” idan aka yi amfani da su kan shingaye irin su gadar Kerch, wadda ta haɗa yankin Crimea da kuma sauran Rasha.

Damar da Amurka ta bai wa Ukraine ɗin za ta kuma saka Birtaniya da Faransa su ma su bai wa Ukraine damar amfani da wasu manyan makamai masu cin dogon zango kan Rasha.

Exit mobile version