Shawarar da zan baiwa Crypto Influencers shine, ba 5K ko 3K yan baiwa suke bukata ba a halin yanzu, ku gina su da ilimi na gaske..
Misali, a maimakon kuyi masu giveaway na 200K ku samu mutum 10 a cikinsu kuyi masu register a makarantar da ake koyar da Crypto kamar Bitkova ko flowdiary, wannan zaisa su koyi trading da sauran ilimin dake cikin crypto wanda zai tallafi rayuwarsu, sannan ku sanar dasu cewa tukuicin da zasu baku shine suma su koyar da wasu abinda suka koya.
Hakan zai taimake su, da yawansu zasu samu damar da sunfi karfin 5K din da zaku raba masu.
Tabbas, anyi kokari wurin raba 200K har zuwa 500K ga yan baiwa, amma dai tabbas idan so ake a gina rayuwarsu dagaske ilimi suke bukata, kuma bawai ilimin da za’a bude whatsApp group ko telegram group ana koyar dasu ba, A’a wanda zasu shiga Aji su koya, register baifi 20K ba, 200K mutum 10 kenan.
Kai kuma dan baiwa, lokaci yayi da yakamata kayi ma kanka karatun natsuwa, ka nemi kudi kayi karatu duk wanda kaga yana samun manyan kudade a crypto space gajiyar ilimi yake ci, shi kuwa influencer koda kuwa bashida ilimin crypto yanada followers da zaiyi influencing a harkar crypto ya samu kudadensa.
Duk wanda yakesonka ba taliya daya-daya zai raba maku ba, yadda ake hadawa zai koyar daku, za’a iya kashe 200K ga mutum 10 idan har zata gina rayuwarsu, babu bukatar kashe 200K ga mutum 40 da cikin kwana biyu amfaninta zai kare.