Abinda zai kara baka mamaki a nigeria shine, duk wata hanya da za’a magance matsalar tsaro sun durkusar da hanyar.
–Jami’an tsaro ba’a tanadar masu sabbin fasahohi domin yakar yan ta’adda ba, sai dai kullun fito da hanyar da za’a kara wa yan majalissu da sanatoci hanyar samun kudi, da siya masu motoci da makamantansu, kai kace wata tsiya suke tsinana ma nigeria da har suka cancanci irin wannan girmamawar.
–Kusan ko wace kasa idan har jirgin sama yana sauka a kasar zaka samu sunada fasahar “Primary Radars” wacce take detecting duk jirgin saman da zai shigo ta cikin sararin samaniyar kasar, da wannan fasahar za’a hango duk jirgin da zai gitta ko zai shigo sararin samaniyar kasar kuma ana da dama da ikon harbo shi idan har ba’a yarda dashi ba. Shi wannan Primary Radars din yana amfani da radio waves wurin ganowa ko detecting da locating na wurin da jirgin sama yake a sararin samaniya, kuma zai bayar da cikakken imformation akan jirgin, a Nigeria, hukumar Nigerian Airspace Management Agency (NAMA) sune suke da Responsibility na tabbatar da tsaron sararin samaniyar nigeria, da samar da fasahar Primary Radars.
A shakarar 2019, anyi installation na wannan fasahar a jahohi irinsu, Lagos, Abuja, Kano, Port Harcourt, Enugu, amma abinda zai baka mamaki tun shekarar 2020 suka ce wannan fasahar wai ta lalace har yanzu shekaru 4 an kasa gyarawa, hukumar NAMA din ce ta sanar cewa fasahar ta lalace ne saboda karancin kayan aiki da kuma rashin maintenance.
–Hatsarin dake cikin rashin wannan fasahar a nigeria ba karami bane, na farko dai duk wanda zai hau jirgin nigeria zuwa wata kasar sai dai kawai yayi bissimillah ya hau amma babu tsaro kwata-kwata, saboda wallahi rashin Primary Radar matsala ce sosai da zata iya haifar da hatsari na jirgi, Allah ne yake karewa, sannan yana shafar hatta su kansu kamfanonin jiragen, saboda jiragen su zasu dinga shan mai sosai da sauran matsaloli da dama kuma hakan zaisa kudin jirgi yayi tsada idan har a Nigeria zaka hau, shiyasa mukeda masifar tsadar safarar jirgin sama.
–Abu na biyu ana zargin ta’addanci da kashe-kashen rayuka dake faruwa a dajukan dake jahohin Katsina, Zamfara da Sokoto akwai wasu ma’adanai a wurin da barayin gwamnati suke kwashewa, wanda wannan kashe-kashe da aka saka barayi su dinga yi, shi zai dauke hankalin Al’umma akan wadannan dukiyoyi dake cikin kasa, sai a dinga shigowa da jirage ana saukar da mutanen da zasu kwashe Albarkatun yankin batareda an sani ba.
Tunda daman sun dakatar da fasahar “Primary Radars” bare a iya gane wane jirgi ne ya sauka a dajukan, kuma meyasa ya sauka a wurin, sannan kuma suka saka yan ta’adda da zasuyi masu aikin da zai dauke hankali, sai suci karensu babu babbaka.
Wadannan abubuwan suna bani mamaki a Nigeria.
- Manyan Refinery a nigeria har guda 3, amma dukkansu basa aiki, sai an fitar da mai kasar waje sannan za’a tace.
- Primary Radar Systems na Nigeria ya lalace gabadaya tun 2020 an kasa gyarawa.
- An kasa Implementing fasahohin zamani irinsu COMsec Settlite, Electronic Security, domin magance matsalar tsaro.
Kuma wai har kace babu sa hannun gwamnati a ta’addanci da kashe kasarmu Nigeria..?
Akwai Allah..