DEGEN (Degenerate) Trading na nufin duk wani Trading da yake da Risk tare da ROI mai yawa, ba wani sabon abu bane. Idan Risk ya wuce 75% a kowanne Trading toh ya zama
Ana iya yin Degen Trading a gurin 3 a Crypto, ana iya yinsa a:
1. Spot/Trading: Kaje kasuwar tsaye irin su MEXC ka samu coin ɗin da ake Pump and Dump dashi, to kayi Degen trading.
2. Futures/Trading: Kaine kana Futures amma kana iya saka Leverage na 100× ko irin 50×, toh Degen Trading kakeyi.
3. Dex/Trading: Kaine kake Dex Trading, amma kafi gane ka samo coin mai 20k M.C. Idan tayi ruwa kawai rijiya, toh kaima Degen kake yi.
Degen Trading a Spot da Futures Trading yana buƙatar tsakanin kwarewa a Technical Analysis, musamman ma a Futures Trading. Sai kasan me kakeyi sosai ka goge a kasuwar.
Degen Trading a DEX yana buƙatar sanin Market Insight, da kuma gane abubuwa irin su Onchain Metric. Sannan kuma mafi amfani ma Dagen ɗin Dex shine ka zama insider.
Dan haka Degen Trading is not only referring to Dex Trading, duk wani Trading mai High Reward da High Risk sunan sa Degen. Ko a Crypto ko a Forex, hasali ma kalmar Degen ɗin yan Futures ne suka fara amfani da ita.
Sabon ɗan crypto wanda bai nuna ba baya Degen, idan ba haka ba zai gane Allah da girma yake.
Yaddda Kasuwar dex take aiki
Kasancewar mutane na saye da sayarwa ne a decentralized exchanges ba a ƙarƙashin gudanarwar hukumomin kasuwannin, mai karatu zai so
ya san yadda mutanen da ke zaune a ƙasashe daban-daban za su iya haɗuwa a wata kasuwa su yi kasuwanci ba tare da kasuwar na sanya ido
akansu ba, kuma ya kasance an yi an gama ba tare da wani ya cuci wani ba.
Decentralised exchanges na aiki ne ta hanyar amfani da tsaruka kamar haka:
No Sign up & KYC
Decentralized exchanges ba su da tsarin yin rijista ko buɗe asusun ajiya,
suna ba wa mutane damar amfani da su ba tare da sun yi rijista ko sun
buɗe asusun ajiya ba. Kamar kasuwanninmu ne na zahiri, inda za ka iya
shiga ka yi sayayya ba tare da ka yi rijista ba domin babu wata hukuma a kasuwar da ke kula ko tantance masu saye da sayarwa.
Connect Your Wallet
Decentralized exchanges ba su da tsarin buɗe asusun ajiya wanda mai
saye zai ajiye kuɗinsa a ciki mai sayarwa kuma ya ajiye abin da zai sayar
a ciki, maimakon haka kowa zai yi amfani da wallet ɗinsa ta musamman
ne da ya ke da ita. Kasuwannin da kamfanonin da su ke samar da wallet
suna ba wa masu sayayya damar jona wallet nasu da kasuwar. Hakan na
nufin, abin da za ka yi amfani da shi a matsayin kuɗin sayayya da kuma
cryptocurrency ɗin da ka ke son sayarwa duka za ka ajiye su a cikin
wallet ɗinka ta musamman ne, idan ka shiga kasuwar sai ka jona wallet
ɗin da kasuwar. Kamar dai yadda ya ke idan za ka je sayayya a wani
shago da ke a kasuwanninmu na zahiri, za ka ta fi da kuɗinka ne a
aljihunka sannan shi kuma mai shagon zai ajiye kayan da ya ke sayarwar
a shagon, idan ka saya ka biya sai a ba ka kayan ka tafi.
*Place An Order*
Bayan ka jona wallet naka da kasuwar, abu na gaba da za ka yi shi ne za
ka zaɓi abin da ka ke son saye ko sayarwa, ka sanya adadin da ka ke son
saye ko sayarwar sannan ka danna alamar saye ko sayarwa. Kamar yadda ya ke a zahiri, idan ka je shago za ka nuna abin da ka ke so ne kuma ka faɗi adadin da ka ke so, kai kuma a faɗa maka kuɗin ka biya.
Smart Contract Automates Trading Bayan ka zaɓi abin da ka ke so kuma ka danna alamar buƙatar saye, abu na ƙarshe shi ne a zare jumillar kuɗin cryptocurrency ɗin da ka saya daga wallet naka sannan a sanya maka cryptocurrency ɗin da ka saya a cikin wallet naka, hakan na faruwa ne da taimakon tsarin smart
contract.
Decentralized Exchange (DEX) .
Decentralised exchanges nau’ikan kasuwannin cryptocurrency ne da ke
ba wa Ƴan kasuwa damar su yi cinikayya a tsakaninsu ba tare da sa hannun hukumomin kasuwar ba.
Hakan na nufin; mai saye zai sayi cryptocurrency ɗin da ya ke so kai tsaye daga mai sayarwa, mai sayarwa
zai sayar da cryptocurrency ɗinsa kai tsaye ga mai saye ba tare da hukumomin kasuwar sun shiga tsakaninsu domin sasantawa ko tantancewa ba.
Irin waɗannan nau’ikan kasuwannin sun fi kama da
kasuwanninmu na zahiri inda mai saye ke shiga ya ga kayan da ya ke so
kuma ya saya a gurin mai sayarwa kai tsaye.
A ‘Centralized exchanges’ hada-hadar cryptocurrency a cikinsu yana
faruwa ne tsakanin mutane uku; mai saye, mai sayarwa da kuma
kasuwar. Mai saye ba ya sayen cryptocurrency kai tsaye daga mai
sayarwa sai dai ya buƙaci kasuwar ta saya masa, mai sayarwa ba ya
sayar da cryptocurrency ɗinsa kai tsaye ga mai buƙatar saye sai dai ya
buƙaci kasuwar ta sayar masa. Amma a decentralised exchanges mai
saye da mai sayarwa ne su ke cinikayya a tsakaninsu, mai saye ya saya
kuma ya biya mai sayarwa kuɗin cryptocurrency ɗin da ya saya, sannan
mai sayarwa ya ba wa mai saye adadin cryptocurrency ɗin da ya sayar
masa.
DARASI GAMEDA DEXS TRADING
Sanin kan mu ne akasarin Coins ɗin da muke Trading dasu a DEXs Sabbin Ƙyanƙyasa ne da yawan su ko Price basu fara nunawa a Wallet ɗin mu ba,kawai muna amfani da DEXs Tools ne wurin ganin Price da kuma Adadin MARKETCAP ɗin su,Wannan dalilin yana daga cikin dalilan da suka sanya Token ɗin basa Respecting na Candlestick Patterns Dan haka babu buƙatar koda yaushe sai mun duba Candlestick Patterns yayin Trading a DEXs
A yadda kasuwar Cryptocurrency take a yanzu Manipulation yayi yawa,wajibi ne ka nemi wasu Strategies na shiga Kasuwar domin yin Trading Musamman DEXs Trading yafi Risk akan CEXs Trading a fahimtar mafi yawan Traders.
bayan na duba Token sosai naga Ingancin sa musamman Liquidity Locked,Burned,Buy tax and Sell tax,Sellebale or Honeypot,Holders and Investors,Community and Shilling,a ƙarshe na kan Duba Source Code domin tabbatar da Security na token,duka waɗannan research na kan yi su Under 20 Minute ne,Sai kuma nayi amfani da…
Strategies na “SCALPING TRAD