LAFIYA UWAR JIKI……
Ko Kun San Amfanin Ganyen Gwanda A Jikin Dan Adam?
Ganyen gwanda na kumshe da sinadiran lipid, calcium, iron, bit C, bit B6, folate, Thiamine, magnesium, phosphorus, potassium, sodium, zinc, Bit A, bitamin E, Bitamin D, D2, D3, Niacin da sauransu. Ganyen gwanda na habaka garkuwar jikin dan’adam.
Su dai garkuwar jiki su ne, ke zama a matsayin sojojin da ke yaki da abokan gaba waton suna yaki da kwayoyin cuta a jiki, dan haka idan suka karamta ko su ka yi rauni to a hakika jikin dan’adam zai raggwanta kuma zai iya fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka daban-daban.
A dalili da haka akwai bukatar jikin dan’adam ya samu garkuwar jiki masu karfin gaske dan su iya baiwa jiki kariya daga abokan gaba. Domin samun wannan damar to sai a lazimci amfani da tsirran itatuwan da kimiyya ta bada tabbacin cewa suna taimaka wa garkuwan jiki ciki harda gwanda.
Ganyen gwanda na kashe cututtukan fata sanadin samun sinadirin karapain a cikinsa wanda wannan ke da tasirin kawar da fungal infections. Ganyen gwanda na maganin gyambon ciki, sai a nemo ganyen gwanda a wanke a shanya idan ya sha iska sai a sabe a sanya ruwan dumi masu kyau kamar misalin rabin kofi madaidaici, sai a tarfa zuma kadan a sha da safe kullum bayan an karya.
Ganyen gwanda na kashe tsutsotsin ciki. Ganyen gwanda na maganin ciwon gabobin jiki da jijiyojin jikin dan’adam sabili da samuwar sinadirin chymopapain. Ganyen gwanda na warkar da cututtukan ciki da kumburin ciki da matsalolin da suka shafi na hanjin ciki. Ganyen gwanda na wanke kazamta da wani abu mai cutarwa da ya yi laulayi a kan babbar hanji.
Ganyen gwanda a binciken wani masani da ke a kasar Japan mai suna Dr. Nam Dang da shi da abokan aikinsa sun tabbatar da cewa ganyen gwanda na dauke da wasu sinadiran da ke kashe kwayar cutar ciwon daji. Baya ga haka, shi kuma Gajowik A, a bincikensa ya gano wani sinadiri (lycopene) mai kashe kwayar cutar ciwon daji, a dan haka ganyen gwanda na maganin ciwon daji.
Diyan gwanda na kara lafiyar zuciya dan samuwar bitamin A, C da E a cikinsa masu taimakon kare afkuwar matsaloli kamar su ciwon suga dana hanyoyin jini har zuwa na zuciya.
Ganyen gwanda na da sinadiran papain da chymopapian masu rage kumburi a sassa da dama na jikin dan’adam a binciken Molecular Nutrition and Food Research. Ganyen gwanda na sanya laushin bayan-gari idan ya yi tauri da yawa kamar na dabbobi.
Ganyen gwanda na narkar da sinadiran cholesterol da yawansu a jiki illa ne matuka musamman ga zuciya, bitamin E da C da ke a ciki suna taimakawa don hana kitsen daskarewa a kan hanyoyin jini.
Ganyen gwanda na maganin basir mai tsiro da gudawa. Ganyen gwanda na maganin kornafi. Ganyen gwanda na maganin malaria a sanadin sinadirin Acetogenin da ke a cikin sa. Ganyen gwanda na maganin ciwon hanta.
Gargadi kada mai juna biyu ta yi amfani da ganyen gwanda domin yana motsa mahaifa. Yawan shan ruwan ganyen gwaiba na haifar da ko dai ganin juyuwa ko zafin ciki da makamantansu a dan haka sai a san yanda za a sha.