Yadda Sabon Tsarin Haraji Zai Gina Tattalin Arziƙin Arewa

Yadda Sabon Tsarin Haraji Zai Gina Tattalin Arziƙin Arewa.

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Sabon ƙudirin neman sauya fasalin tsarin biyan haraji da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aikewa majalissar ƙasa ya janyo cece-kuce musamman a Arewa, inda mutane suke kallon abun a matsayin wani abu mai wahala wanda zai shafi tattalin arziƙinsu, sai dai kuma, a ɗan nazarin da na yi bayan tattaunawa da masana da ƙwararru a fannin, na fahimci cewa idan har ƴan Arewa musamman ma gwamnoninmu za su ɗauki abun da muhimmanci to mu ne za mu fi kowa cin gajiyar sabon tsarin idan ya tabbata.

Dalili a nan shi ne: cikin tanadin sabon tsarin, kaso 60 cikin ɗari na abin da aka samu za a raba shi ne bisa abin da kowace Jiha ta tara, sai kaso 20 da za a raba bisa lura da yawan al’umma, sannan sauran kaso 20 kuma za a raba shi ne daidai da daidai a tsakanin Jihohi. Sannan kuma, mafi yawan harajin za a tatso shi ne daga mutane ko wuraren da ke sayen kaya ba wai daga wurare ko kamfanonin da ke samar da kayan ba.

Sanin kowa ne muna samar da kayayyaki irin su kayan miya da dabobi irin su raguna da shanu a kai su Kudu a cikin tireloli, kuma mutanenmu suna tafka manyan asarori idan suka fita da kayan aka samu lalacewar mota a hanya ko idan kayan ba su ƙare da wuri ba, kenan idan muka samar da kamfanonin da za mu riƙa sarrafa kayayyakinmu a Arewa muna fita da su Kudu a zamanance, za mu ragewa kanmu asarar da muke tafkawa, sannan kuma za mu fi kowane yanki cin ribar wannan sabon tsafin haraji a Najeriya duba da cewa tattalin arziƙinmu zai bunƙasa, kuma ɗumbin matasa da ba sa aiki za su samu ayyukan yi.

Duba da haka, zan iya cewa idan har tsarin ya tabbata to hakan ba ƙaramin cigaba ba ne a Arewa. Domin kuwa gwamnatocin Jihohi da masu hannu da shuni za su buɗe wuraren sarrafa kayayyakin da muke samarwa a Arewa ta yadda za a yi musu tsari irin na zamani ana fita da su Kudu wanda hakan zai buɗewa matasa hanyoyin samun guraben ayyukan yi gami da bunƙasa tattalin arziƙinmu. Harajin da za a riƙa tatsa zai na fitowa ne daga Kudu inda ake kai kayayyakinmu. Idan gwamnatin tarayya ta tara haraji zai zamto mu ne za mu fi samun kaso mai yawa duba da cewa mun samar da kamfanoni ga kuma yawan al’umma.

Exit mobile version