content="218a3834dd422f26d2be19ac5e7d243b"/> Yadda zazzafar muhawara ta kaure tsakanin Barau Ndume a majalisa kan kudurin dokar haraji na Tinubu - Samaniya Report News
LABARAN DUNIYA

Yadda zazzafar muhawara ta kaure tsakanin Barau Ndume a majalisa kan kudurin dokar haraji na Tinubu

An samu takaddama mai zafi a majalisar dattawa yayin da Sanata Ali Ndume ya yi martani ga Mataimakin Shugaban Majalisar, Barau Jibrin, kan kokarin gayyatar kwararru kan haraji da jami’an gwamnati zuwa zauren majalisa ba tare da sanarwa ba.

Rikicin ya ta’allaka ne kan Dokokin Gyaran Haraji, inda wasu ƴan majalisa daga yankin arewa suka bayyana rashin amincewarsu.

Rikicin ya fara ne lokacin da Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Opeyemi Bamidele, ya sanar da wani ba-zata game da dakatar da ajandar ranar don bai wa kwararrun haraji da jami’ai, ciki har da Shugaban Hukumar FIRS, damar gabatar da jawabi ga ‘yan majalisa kan Dokokin Gyaran Haraji da ake takaddama kansu.

Duk da haka, Sanata Abdul Ningi ya nuna adawa da hakan bisa ka’idojin Majalisar Dattijai. Ya ce ka’idojin ba su ba da izini ga kowa ya yi magana a zauren majalisa ba sai tsoffin Shugabannin Kasa, tsoffin Shugabannin Majalisar Wakilai, da tsoffin sanatoci. Ningi ya jaddada cewa irin wannan bayani daga kwararru ya dace a yi shi ne a matakin kwamitocin majalisa, ba a taron majalisar gaba daya ba, kasancewar dokokin majalisar ba su amince da irin wannan ba.

Sanata Barau Jibrin, wanda ke jagorantar zaman majalisa, ya mayar da martani ta hanyar cewa Dokokin Gyaran Haraji suna da muhimmanci ga kasa kuma tuni Majalisar Wakilai ta yi aiki a kansu. Ya yi bayanin cewa bai wa kwararru damar yin magana a zauren majalisar zai taimaka wa ‘yan Najeriya su fahimci abinda dokokin suka kunsa. Daga nan sai ya yi fatali da maganar Ningi.

Sanata Ndume, cikin bacin rai, ya fada wa shugaban zaman majalisar da cewa, “Za ku iya cimma muradinku, amma ni zan yi magana.” Ya kuma kara da cewa, “Za ku iya amfani da guduma, amma ni zan yi amfani da muryata.”

Rikicin ya dada ta’azzara lokacin da Sanata Ndume, cikin takaici, ya jagoranci wasu ‘yan majalisa daga arewa wajen ficewa daga zaman majalisar a matsayin alamar rashin jin dadi game da take dokar majalisa.

Bayan roko daga Shugaban Marasa Rinjaye da wasu abokan aikinsa, Ndume da sauran sanatocin da suka fita suka koma zauren majalisa.

Da suka dawo, Ndume ya sake daukar mataki ta hanyar yin magana bisa ka’ida, yana neman Mataimakin Shugaban Majalisa Barau ya ba shi hakuri saboda zarginsa da yin magana ba tare da hujja ba.

Amma Barau ya sake yi masa fatali da maganarsa, sannan aka ci gaba da bai wa kwararrun haraji damar yi wa sanatoci bayani kan Dokokin Gyaran Haraji, duk da adawar da aka yi.

Rahoton Daily Nigerian Hausa

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button