Ba Bakwana yakamata a kama ba, masu masa Bidiyo daga Kwankwasiyya da Gandujiyya yakamata a kama.
Daga: Haji Shehu
Yanzu nake ganin wani Bidiyon dake nuna cewar an kama Bakwana saboda ya zagi Kwankwaso, idan har wannan Bidiyo ya tabbata gaskiya, ko shakka babu gwamnatin Abba bata shirya juriyar Adawar da gwamnatin Ganduje ta jurewa ba.
Ba kalan zagin da Bakwana bai yiwa Ganduje ba a lokacin da yake Mulki, amma haka gwamnatin Ganduje tayi kamar bata san yana yi ba saboda kowa yasan yana da matsala ta Kwakwalwa.
Ba Bakwana yakamata a kama ko ayiwa barzana ba, mutanen da suke mas Bidiyo su yakamata a kama idan har da gaske gyara akeso ayi, kuma mutanen dake masa Bidiyon nan akwai su a kowacce tsagin siyasar jihar Kano.