Site icon Samaniya Reporters

Ayi amfani da wani sashe na Albashin sanatoci a biya bukatun da akeson biya da naira 50 din da akeson karba ga talakawan da suke neman kudi domin su rayu

—Ana biyan sanatocin nigeria albashin naira 750,000 duk karshen wata, sai kuma allowances idan aka hada duka alawus din gabadaya zai kama 13.5 million naira a duk karshen wata. Albashi 750,000 + Alawus 13.5 a duk wata.

—Wanda a lissafe duka zai kama 14.25 million naira duk karshen wata, ko kuma kace 171 million naira duk shekara.

—Sanatocin nigeria suna cikin mutanen da suka fi samun kudi a bangaren siyasa a duk duniya. misali, Sanatocin kasar america suna samun dallar amurka $174,000 duk shekara, wanda idan muka converting kudin da kudin nigeria a farashin 1, 700 duk dollar zai kama: 295,800, bai kai albashin sanatocin nigeria ba.

—Sanatocin nigeria suna karbar abinda ake kira da “Constituency Fund” na 200 million naira, wanda ana basu kudin ne suyi amfani dasu wurin yiwa Al’ummar da suke wakilta ayyuka. (Ba lallai suyi ayyukan ba)

—Wadannan kudaden da ake baiwa sanatoci idan da za’a rage su, ayi amfani dasu wurin gina kasar mu, da inganta masana’antu da tattalin arzikin kasar mu da ba sai sun karbi 50 naira a wurin talakawan da kullun fafutuka suke domin su rayu ba. A karbi kudaden su ayi abinda akeso ayi da 50 naira din mu.

Abar talakawa su rayu..🙏

Exit mobile version