Site icon Samaniya Reporters

YANZU-YANZU: Ƙudirin Dokar Sauya Tsarin Haraji: Ƙungiyar Kare Muradun Jihar Kano Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Sanata Barau Ta Kuma Yi Gargaɗi Da Jan Kunne Ga Sanata Ali Ndume

Domin kuwa a bayyane take cewa Sanata Barau Jibrin ya taka rawa ne a matsayin shugaba da ke jagorantar zaman, ya kuma karanta takarda ne wacce hukumar tattara haraji ta ƙasa, FIRS ta gabatar musu kan ƙudirin sauya tsarin haraji. Yayi aikinsa ne a matsayin shugaba ba wai ƙudiri ya gabatar ko goyon bayan wani ƙudirin yayi ba.

Cikin jawabin da ta fitar kamar yadda Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu rahoto, ƙungiyar ta cigaba da cewa, ya kamata a fahimci cewa Sanata Barau ba shi ne ya gabatar da ƙudirin ba, kuma bai bayyana ra’ayinsa a kai ba ya dai bi tsarin da ake bi ne wajen ba wa shugaban kwamitin sauya fasalin harajin, Mista Taiwo Oyedele da sauran ƙwararru dama su gabatar da jawabi a gaban zauren majalissar. Kuma irin wannan gabatarwa aka yi a gaban zauren majalissar wakilai da gaban ƙungiyar gwamnoni batare da an samu irin wannan ruɗani ba.

Ta cigaba da cewa, a ƙoƙarin Sanata Barau na ganin an tabbatar da adalci da ba wa kowa dama, ya ɗauki nauyin wayar da kawunan al’umma cikin manyan Harsunan Najeriya na Hausa, Ibo, Yoroba da sauran harsuna tayadda ƴan ƙasa za su fahimci haƙiƙanin yadda ƙudirin dokar yake da duk wasu abubuwa da ka iya biyo bayansa.

“Duk da cewa muna girmama ƴancin faɗin albarkacin baki, sanata Ndume yana da ƴancin faɗar abin da yake so, amma kalmomin da yayi amfani da su a zaman majalissar ba daidai ba ne kuma manufa ce ta ƙirƙirar bayanan da ba na gaskiya ba. A madadin ya bi matakin da ya dace sai ya zaɓi ƙalubalantar Sanata Barau domin ya karkatar da hankalin al’umma su yi zaton cewa Sanata Barau yana da hannu wajen goyon bayan ƙudirin adawa da Arewa”. Cewar ƙungiyar.

Abin takaici, wannan lamari ya shafawa Sanata Ndume baƙin fenti kan kallon Gwarzo da ake masa a Arewa tare da zargin Sanata Barau batare da haƙƙi ba. Wannan halayya ta zubar da kimar majalissa tare da dasa ƙiyayya da rarrabuwar kawuna a tsakanin ƴan Najeriya.

Ƙungiyar ta kuma ƙara da yin gargaɗi da jan kunne ga sanata Ndume da ya daina amfani da wannan taƙaddama ta ƙudirin gyaran tsarin haraji a matsahin makamin da zai ɓatawa sanata Barau Jibrin suna. Tare da yin ƙira ga al’umma da su nemi cikakken bayani a kan ƙudirin dokar gabanin su ce komai a kai domin har yanzu ƙudirin yana gaban zauren majalissar ana cigaba da bibiya da nazari mai zurfi a kai gabanin a sake dawo da shi zaman majalissar nagaba.

A cewar ƙungiyar, wannan yanayi na siyasa yana buƙatar shugabanni su sanya hikima da dabaru wajen tunkararsa tare da magance bayanan da ba na gaskiya ba. “Muna kira ga dukkan sanatoci ciki har da Ndume da su bi matakin tattaunawa tare da maida hankali kan abin da zai fi zama masalaha ga ƴan Najeriya. Sanata Barau a kowane lokaci mutum ne mai daraja da martaba a Jihar Kano da Arewa, kykkyawan tarihinsa a bayyane yake, ba za mu taɓa barin wani mutum ya ɓata masa suna saboda neman cimma wata manufa ta siyasa ba”.

Menene ra’ayinku?

Exit mobile version