Site icon Samaniya Reporters

Yarinya ‘Yar Shekaru 12 Za Ta Fuskanci Shari’a

Kasashen Ketare: Yarinya ‘Yar Shekaru 12 Za Ta Fuskanci Shari’a Kan Zarginta Da Kishe Kakanta.

Kasashen Ketare: Yarinya ‘Yar Shekaru 12 Za Ta Fuskanci Shari’a Kan Zarginta Da Kishe Kakanta.Daga Auwal Isah Musa.Wata Yarinyar ‘yar kimanin shekaru 12 da haihuwa da ba a bayyana sunanta ba saboda dalilai na shari’a, za ta gurfana a gaban kotun majistare ta matasa wadda ke da zamanta a yankin Leicestershire da ke birnin Braunstone na kasar Ingila a ranar Litinin mai zuwa.Hukumar ‘Yansandan yankin Leicestershire ne suka shigar da karar zargin kisan a gaban kotun, suna tuhumar yarinyar da laifin kashe kakanta mai shekaru 80.Tun da farko dai, zargin ya soma ne kan wani yaro dan kimanin shekaru 15, wanda a da aka bayyana cewar zai bayyana a kotun Leicester Crown a karshen wannan makon. Amma wasu bayanai sun ce an dage sauraren karar tun a watan da ya gabata, inda aka bayyana cewar za a fara shari’arsa a watan Fabrairun badi.Dattijo, Bhim Kohli, an tsince shi ne ayashe a ranar 1 ga Satumban 2024 a yayin da yake tafiya da Karensa a filin shakatawa na Franklin, kusa da gidansa a garin Braunstone, da ke lardin Leicestershire, inda aka hanzarta kai shi cibiyar kiwon lafiya ta Sarauniya a Nottingham, washegari kuma ya ce “ga garinku nan.””Bhim miji ne abin kauna, uba kuma kaka. Ya kuma kasance da, kane kuma kawu.””Ya kaunaci jikokinsa da dukkan zuciyarsa, sannan yana son zama tare da su.”Hakika ya kasance mutum mai nuna soyayya, mai kula, wanda rayuwarsa kacokaf ya karkatar da ita ga Ahalinsa.” -Wasu zantukan da Ahalinsa suka bayar a kansa.A hoto, Dattijo Bhim Kohli ne yake nisahdi da Ahalinsa.

Daga Auwal Isah Musa.

Wata Yarinyar ‘yar kimanin shekaru 12 da haihuwa da ba a bayyana sunanta ba saboda dalilai na shari’a, za ta gurfana a gaban kotun majistare ta matasa wadda ke da zamanta a yankin Leicestershire da ke birnin Braunstone na kasar Ingila a ranar Litinin mai zuwa.

Hukumar ‘Yansandan yankin Leicestershire ne suka shigar da karar zargin kisan a gaban kotun, suna tuhumar yarinyar da laifin kashe kakanta mai shekaru 80.

Tun da farko dai, zargin ya soma ne kan wani yaro dan kimanin shekaru 15, wanda a da aka bayyana cewar zai bayyana a kotun Leicester Crown a karshen wannan makon. Amma wasu bayanai sun ce an dage sauraren karar tun a watan da ya gabata, inda aka bayyana cewar za a fara shari’arsa a watan Fabrairun badi.

Dattijo, Bhim Kohli, an tsince shi ne ayashe a ranar 1 ga Satumban 2024 a yayin da yake tafiya da Karensa a filin shakatawa na Franklin, kusa da gidansa a garin Braunstone, da ke lardin Leicestershire, inda aka hanzarta kai shi cibiyar kiwon lafiya ta Sarauniya a Nottingham, washegari kuma ya ce “ga garinku nan.”

“Bhim miji ne abin kauna, uba kuma kaka. Ya kuma kasance da, kane kuma kawu.”

“Ya kaunaci jikokinsa da dukkan zuciyarsa, sannan yana son zama tare da su.

“Hakika ya kasance mutum mai nuna soyayya, mai kula, wanda rayuwarsa kacokaf ya karkatar da ita ga Ahalinsa.” -Wasu zantukan da Ahalinsa suka bayar a kansa.

A hoto, Dattijo Bhim Kohli ne yake nisahdi da Ahalinsa.

Exit mobile version