Yadda Mahadi Shehu Yayi Zargi, -Rahoton Bincike
Sojan Da Aka Gani Cikin Bidiyo Da Kayan Sojojin Ƙasashen Waje Sòjaɲ Birtáɲiya Ne Ba Sojań Faráɲsa Ba Ne Kamar
Biyo bayan fitar wani bidiyo ɗauke da fuskar wani sojáɲ ƙasar waje inda Mahadi Shehu yayi zargin céwa sojojiɲ ƙasar Faraɲsa sun fara kafa sansaɲi a Najeriya dòmin yaƙi da Bòkô Hárąm musamman a yankun Maiduguri, Sokoto, Zamfara, da Jihar Kogi, bincike ya tabbatar da cewa zargin ba gaskiya ba ne.
A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, Birgediya Janar Haruna ne yake magana da manema labarai a cikin bidiyon, a yayin da yake ganawa da Kanal Martin Leach, kwamandan rundunar tawaga ta musamman da ke aiki kan harkokin horar da sojoji da ke aikin ƙarfafa alaƙa a tsákanin sojojiɲ Najeriya da na Birtaniya.
Ko da a watan Maris na shekarar 2024, Kanal Leach ya jagoraanci tawagar sojojin Birtaniya sun ziyarci kwamandan makarantar horar da sojoji ta Najeriya, Janar JO Ochai, a hedikwatar makarantar inda suka tattauna kan fannonin ƙulla alaƙar aiki tare.
A lokuta daban-daban Kanar Leach ya sha jagorantar soojojin rundunar tasa zuwa Najeriya kan ayyuka daban-daban na ba da tallafin horon ƙwarewar aiki ga sojojin Najeriya.
“Ba sojojin Fáraɲsa ba ne, idan kuka kalli kayan da ke jikinsu da kyau, za ku ga cewa kayan sojojin Birtaniya ne kuma ba sojojin yaƙi ba ne, sojoji ne da ke aikin ba da horo”. Cewar Birgediya Janar Tukur Gusau, daraktan sadarwa na ma’aikatar tsaro.