MAMAKI
WASU ABUBUWA MASU BAN-
MAMAKI
Daga Idris M Rismawy
••• ALLAHU AKBAR•••
=================
»» Lokacin da aka haifeka za a yi
maka kiran sallah batare da
sallah ba. Lokacin daka mutu shi
kuma za a yi maka sallah ba
tareda kiran sallah ba.
»» Lokacin da aka haifeka za a yi
maka wanka a tsaftaceka
saboda ba zaka iyaba. Haka ma
lokacin da ka mutu za a yi maka
wanka a tsaftaceka saboda ba
zaka iya ba.
»» Lokacin da aka haifeka
iyayenka da danginka zasu yi ta
murna da farin ciki. Amma
kuma lokacin da ka mutu zasu yi
ta kuka da bakin ciki.
»» Yadda baka san wanda ya
daukoka daga mahaifa ba
lokacin da zaka fito duniya.
Haka ma a lokacin da ka mutu,
ba zaka san wadanda zasu
daukeka ba zuwa kabari.
»» Lokacin da kazo duniya baka
zo da komai ba. Haka lokacin da
zaka koma lahira ma ba zaka tafi
da komai ba, sai ayyukanka.
»» KA SANI CEWA AN
HALICCEKA NE DAGA KASA.
TSARKI KUMA YA TABBATA GA
WANDA ZAI MAYAR DA KAI
CIKINTA BAYAN
MUTUWARKA»»
===========••••
•••==========
YA ALLAH KASA MU CIKA DA
IMANI. KA HASKAKA
KABARINMU. KA JIKAN
IYAYENMU MATATTUN CIKINSU
DA MASU RAI. YA ALLAH KA
DAUKAKA MUSULUNCI DA
MUSULMAI. KA KASKANTA
KAFURCI DA KAFURAI DA
AZZALUMAI. KUMA KA ZAUNAR
DA KASARMU LAFIYA, AMIN.