CRYPTO WALLET Vs WEB3 WALLET
CRYPTO WALLET Vs WEB3 WALLET:
Crypto wallet: ita ce wallet da muke Amfani da ita wajan ajiye/ɓoye Cryptocurrency’s ɗinmu a ciki.
Sannan wallet da ce take bamu damar:
- Turawa(Sending).
- karɓa (Recieving).
Note: idan Ana magana akan “Crypto wallet” Ka sanin wancan abubuwan da lissafo a sama (STORIN, RECIEVING, SENDING) shine kawai aikin da suke yi. Ba’a siye ko siyar wa a cikin WALLET.
A inda muke Siyan “TOKEN” ko siyar da TOKEN shine kan DEX Ma’ana “Decentralised Exchange” anan ne muke EXCHANGE na Abubuwa, mu bada Dollers$$ a bamu TOKEN/coins ko kuma mu bada TOKEN/COINs a bamu DOLLERS$$.
Fatan An fahimci wannan sosai!?
Zan ajiye link na rubutun da nayi Akan DEX a comment. Ina ganin idan ka karanta zaka fi fahimta sosai. Duk da Nasan insha’Allah an fahimta😊.
Bari mu cigaba:
A ɓangaren su waɗannan “Crypto wallets” ɗin muna da su kala kala (Types of crypto wallet).
- HOT WALLET (wallet ɗin da suke kan internet a koda yaushe)
Misali: - Web site (Metamask Extension, Trust wallet extension etc.)
- Application ( METAMASK Applicable, Phantom Application, etc.)
- COLD WALLET: Wannan sune wallets ɗin da basa kan Internet:
Misali: - Hardware wallet
- Paper walletwallet
Zan ɗanyi bayanin su a taƙaice saboda kar rubutun yayi tsayi!
- Hardware wallet: Wannan wallet ce ta zahiri, ma’ana dai kana iya taɓa ta (Hardware).
Wannan itace wallet ɗin da tafi ko wacce tsaro. Domin kuwa ba akan Internet take ba. Kana ɗorata aka. Internet kawai idan zaka tura COINs.
Misali:
Idan kana son tura COINS ɗinka dake cikin ta zuwa wani waje. To a wannan lokacin ne zaka ɗora ta akan internet.
Muna da Company’s da yawa da suke siyar da irin waɗannan wallets ɗin:
- SAFEPAL WALLET
- LEDGER WALLET.
da sauransu.
Yadda take yin aiki shine:
Kamar misali “LEDGER WALLET” suna da wani site da ake kira “LEDGER LIVE” da zarar kaje ciki, sai ka zaɓi Blockchain ɗin COIN ɗin da zaka tura, ka zaɓi Adadi da komai da komai. Sai kayi Requesting Signing Transaction ɗin akan wannan Hardware wallet ɗin, sai kayi shikkenan a sauƙaƙe…
Kamar yadda muka sani cewa Wallet da muke Amfani dasu yau da gobe, irin su METAMASK ba ko wane coins suke ajiye ba. Kamar dai misali, kasan cewa METAMASK bata supporting duk wata BLOCKCHAIN wanda ba EVM-compatible.
Kamar irin su $BTC $SOL $TRON. Duka wannan bazaka iya ajiye a METAMASK ba. Saboda ba EVM-compatible bane.
To suma haka suke Wasu daga cikin waɗannan Hardwear wallets ɗin ba ko wane COIN/BLOCKCHAIN suke Amin cewa dashi ba, Wasu zaka ga iya BTC, ETH, XRP, DOGE. Supporting. Wasu kuma duka.
Don haka yana da kyau ka duba akwai Token da kake son Ajiye kafin ka siya!!.
- HOT/software WALLET: wannan sune wallet ɗin da a koda yaushe suna kan Internet. Kamar irin su METAMASK, TRUST WALLET, PHANTOM. da sauran su.
Waɗannan wallet ɗin suna aiki ne akan internet, don haka Private keys ɗinka suna kan Internet.
Suna da daɗin Amfani musamman wajan tura COIN ba kamar Hardware wallets ba, domin duk lokacin daka bukaci ka tura kawai shiga zakayi ka tura. Baka buƙatar sai kayi ɗora su akan internet.
To Amman tayaya “HARDWARE WALLET” suka fisu tsaro!?
Mun sani cewa ana iya HACKING WAYAR mutun, ta kan internet. Sannan a iya kwasar duka bayanan na cikin wannan wayar. kaga kenan duk lokacin da akayi Hacking ɗin wayarka za’a iya zuwa a satar maka Private keys ɗinka. To Amman idan basa kan internet fah!?
Kasan babu yadda za’ayi a iya HACKING ɗinsh😊.
- Paper wallet: Wannan wallet ce ta takarda.
Da yawa mutanen mu idan sukaji Ance Paper wallet Abun da yake fara zuwa kansu shine, wata Lafiyayyar takarda da hotan BITCOIN a jiki😂.
Ko takardar jarida ka samu ka rubuta Private keys ɗinka a jiki, to wannan Takardar ta zama wallet domin kuwa idan wani ya sameta zai iya cire kuɗinka.
Idan ta ɓata kuɗinka sun ɓata.
Duk inda ka rubuta keys ɗinka wajan ya zama wallet.
Abun da ya kamata ka sani a koda yaushe shine:
“NOT YOUR KEYS, NOT YOUR ASSET”.
WEB3 WALLET:
Web3 wallet: itace wallet ɗin da ake Amfani da ita wajan ajiye abubuwa da dama.
kamar irin su:
- NFTs(Non-fungible token).
- Metaverse: ƙirƙirar riyar duniya da ake shirya ta akan Blockchain.
- Dama su kansu Cryptocurrency’s ɗin. Da sauran wasu muhimman abubuwa da dama da zaka ajiye akan Blockchain. kamar dai yadda muka sani cewa BLOCKCHAIN TECHNOLOGY is beyond CRYPTOCURRENCY….
Shi web3 shine Next Evaluation na WEB da zamu shiga(Ko kuma ince muke ciki), kuma Blockchain Technology itace system guda ɗaya da a yanzu take cika wannan tsari, na bawa mutun damar mallakar bayanan sa, da komai da komai da yake so akan internet.
Fatan An fahimci bayanin sosai.
Idan akwai abun da ya shige maka duhu kayi Tambaya 😊.
Idan ka ƙaru, kayi sharing zuwa gaba domin wasu ma su Amfana!
Forfor Tech Tube