content="218a3834dd422f26d2be19ac5e7d243b"/> MENE NE SMART CONTRACT AUDIT - Samaniya Report News
BLOGGER

MENE NE SMART CONTRACT AUDIT

MENE NE SMART CONTRACT AUDIT (1)

Lafazin smart contract audit na ishara zuwa ga wani hurumi na tsarin binciken kwakwaf na kokarin nazarta da gano nakasu ko tangarda da masu bincike ke yi “auditors” a cikin madarar bayanan umarni na harshen na’ura mai kwakwalwa “codes”.

Manufar aiwatar da wannan bincike shine domin a gano inda ke da rauni “vulnerabilities” tare da tabbatar da an gyatta shi domin aiki yadda ya dace.

img 20241123 wa0010
img 20241123 wa0010

Smart contract audit tsarin nazariyyar bayanan umarnin kwamfuta ne “code review” ta fuskar ingancin tsaro na fasahar smart contract. Muradin mai bincike shine samun wasu kura-kurai masu yawa “bugs” tare da fadakar da abokan hulda yadda za su inganta tsaron wannan fasaha ta smart contract ko kuma muhallin da ke dauke da curin bayanan umarni “codebase”.

Smart contract audit ya kunshi gudanar da bincike layi-bayan-layi “line-by-line analysis”, gane yadda bayanan umarni (codes) ke dabi’antuwa yayin da suke fuskantar matsi da kuma irin tawaya da za ta same su “stressing”, aiwatar da gwaje-gwaje “testing”, tare da fahimtar ita kan ta smart contract din ko bigiren da ke dauke da yambun bayanan umarni “codebase” ta hanyar amfani da fikirarka ta Banu Adam “manual review” ko ta hanyar amfani da wata manhaja domin gane kwazo ko rauninsu “automated test”.

Wannan na taimakawa wajen ganin an samar da tsaro tare da inganta dogaro da fasahar smart contract domin magance mummunar ta’adar nan da miyagu ke yi ta kirkirar wata masarrafa “software” dake kutsa kai cikin na’urorin mutane domin shigar da wasu bayanai masu cutarwa “software exploitation” da kuma kiyaye hasarar kudaden jama’a “fund loss”.

Akwai nau’ukan bincike a wannan sashe masu yawa “audits” kamar, competitive audits, inda dubunnan masu bincike a fannin tsaro da lafiyar bayanai “security researchers” ke baje-kolin fikirarsu tare da yin gasa da junan su wajen gano inda bayanan umarni (codes) ke da wata matsala.

Har ila yau, akwai private audits, inda wasu zababbun gungun masana tsaron na’ura mai kwakwalwa ke aiki da junansu bisa ka’idojin kamfanin da ya dauke su aiki domin tabbatar da fasahar smart contract ta wannan kamfani da kuma abokan huldarsu na cikin aminci.

Ganin irin yadda fasahar blockchain ke kara samun tagomashi daga al’ummomin duniya, bukatar samuwar yalwa ta masu aiwatar da irin wannan aiki na karuwa.

Ta hanyar koyon smart contract auditing, za ka samu kudi, bugu da kari, za ka bada gudunmowa wajen tsaftace muhallin Web3 tare da inganta tattalin arziki na wannan sashe.

Show More

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button