“Allah maɗaukakin sarki ya laburta mana yadda kowa yake yin takansa a ranar ƙiyamah, kowa burinsa idanma kowa zai halaka to shi ya tserata. A ranar ne uwa za ta ajiye ɗan da ta haifa, uba zai guji matarsa da ƴaƴansa, a ranar shima ta kansa yake babu batun ya taimaki iyalinsa”
“Ranar da mutum yake gudu daga ɗan-uwansa, da uwarsa da ubansa, da matarsa da ɗiyansa, ga kowane mutum daga cikinsu, a ranar nan akwai wani sha’ani da ya ishe shi” (Surah Abasa)
“A ranar lahira kowa yakan zamto neman takansa yake yi, babu mai lura da halin da ɗan-uwansa yake ciki, kowa burinsa ya samu tsira a wannan ranar. Ɗan-uwa yakan guji ɗan-uwansa. Ɗa yakan guji uwarsa da ubansa. Uwa takan tsallake ta bar ɗanta. Kowa yakanyi ta kansa ne a wannan ranar, babu mai taimakon wani don wani ya tserata. Haƙiƙa wannan ya ishi mai hankali tashin hankali game da sha’anin wannan ranar”
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used. Visit our Privacy and Cookie Policy. I Agree