Bayan kasancewar “internet” network of networks wato interconnected network kenan kamar yadda na zayyano a rubutuna na baya, sai aka fara tunanin yadda za a samar da wani abu wanda connected devices (na’urorin da suka yi hadakayya da juna) za su iya shiga su gani.
Misali: A wani taron Flowdiary, sai na hadu da dalibai daga courses daban-daban kamar Web Dev., Cybersecurity, da Digital Marketing, kuma kowanne course yana da nasa group din. A lokacin suna tattaunawa a cikin aji, sai na ce bari na kirkiro wani allo wanda duk wanda yake cikin ajin nan zai iya ganin duk wani rubutu ko bayani da zan wallafa.
Haka aka yi, a shekarar 1989 wani Bature mai suna Tim Berners-Lee ya samar da World Wide Web (www), wanda ya kasance wani shafi ne (webpage) da connected devices za su iya shiga su ga abun da aka wallafa a ciki. Sannan aka fadada shi ta yadda ba mutum daya ba ne zai iya mallakar shafi, kowa zai iya mallaka kamar dai a ce an bude jeji kowa ya je ya yanki gona.
Misali na biyu kamar yadda na fara bayani a game da Xender: idan kun yi connecting devices dinku ta Xender kuna sharing files, sai ku ka yanke shawarar bari ku samar da wani shafi (page) a cikin wannan connection din naku, ta yadda duk wanda ya hau connection dinku na Xender zai iya shiga ya ga abun da aka wallafa.
Dalili mai karfi na samar da “web” shi ne don samun damar watsa labarai ta yadda kowa zai iya gani a fadin duniya. Ta wannan hanyar gidajen jaridu suka zamanantar da kansu, wanda yanzu matukar gidan jarida ba shi da website to za a manta da shi ne. Wannan dalilin ya sa yake da matukar kyau muke kiran matasa cewa rinka tafiya da zamani ta hanyar koyon
A wani rubutuna na baya inda na yi bayanin Web 1.0, da Web 2.0, da Web 3.0 na nuna cewa farkon wanda aka samar shi ne Web 1.0 wanda ya kasance inda mutum zai karanta rubutu ne kawai a gidajen jaridu ko wasu shafuka, babu cigaban daura bidiyoyi ko hotuna ko kuma samuwar fasahar social media.
Ina fatan mun fahimci bambancin da ke tsakanin internet da web? Idan ba ka samu bayanin internet ba ka duba rubutuna na baya don samun karin haske.
TAMBAYOYI
1 — Ba mu takaitaccen bayani game da internet?
2 — Me ya sa Tim Berners-Lee ya samar da World Wide Web?
3 — Da me Xender take kamanceceniya: Web ko Internet?
Sai mun hadu a rubutu na gaba…
@forfortechtube