Me ya sa kuɗin-cizo ke da naci?
Bayani kan maƙala
- Marubuci,Jasmin Fox-Skelly
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari,Journalist
- 12 Nuwamba 2023, 04:00 GMT
A halin yanzu Faransa na fuskantar barazana daga mamayar kudin cizo.
A bana, a birnin Paris, an samu rahoton ɓullar kuɗin cizo a makarantu da jiragen ƙasa, da asibitoci da gidajen sinima.
Sai dai annobar na ci gaba da zama wata babar barazana a ƙasar.
A cikin 2020, sai da aka rufe wani sashen da ke cikin wani asibitin Faransa bayan an shigar da wani mara lafiya ɗauke da kuɗin cizo.
An ɗauki matakin rufe sashen ne bayan bincike da aka yi ta amfani da wani kare da aka yi amfani da shi ya nuna cewa kwarin sun mamaye dakuna huɗu.
Rufewar ya ɗauki kwanaki 24, kuma an kashe kusan dalar Amurka 400,000 (£ 333,000) don yin magani.
Hakan ya nuna cewa ƙwarin – waɗanda ba su fi girman ƙwayar shinkafa ba – na zama matsala mai girma a biranen duniya a cikin shekaru ashirin da suka wuce.
Tafiye-tafiye a duniya, sun taimaka wa ƙwarin wurin yawo tsakanin nahiyoyin yayin da suke ɓoye a cikin jakunkunan fasinjojin jirgin da ba su san da zamansu ba.
Wani bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa ƙwarin na da matuƙar wahalar magancewa.
A shekarar 2005, Warren Booth ya kasance matashi mai bincike a Arewacin Carolina, lokacin da ya fara yin wani abu mai ban mamaki.
Ya tuntuɓi kamfanonin masu maganin ƙwari, kuma ya ce su aika masa da samfurin kuɗin cizo na gama-gari, wanda aka fi sani da Cimex lectularius.
Tsakanin 2005 zuwa 2009, ya yi nasarar tattara samfura 161 daga jihohi 38 na Amurka, kowannensu ya samo asali ne daga wata ƙwayar halitta ta daban.
Ya yi niyya ya yi nazarinsu, amma bincikensa ya katse lokacin da Jami’ar Tulsa ta ba shi aiki a matsayin likitan kwayoyin halittu.
Shekara goma sha biyar bayan haka, ya haɗa hannu da ɗalibarsa Cari Lewis da ta kammala karatun digiri, wadda ta tara na’o’in kuɗin cizo guda 233 da aka ɗauka daga jihohin Amurka tsakanin 2018 zuwa 2019.
Sun sami yawan nau’o’in kuɗin cizo masu ban sha’awa. Amma me za ayi da su? Da yake sun kasance masu binciken ƙwayoyin halitta, sai suka fara shirya ƙwayoyin halittar ƙwarin.
Suna binciken sauye-sauyen da ke cikin ƙwayoyin halittar ƙwarin. Wannan na da matuƙar muhimmanci wurin motsawar jikin kuɗin cizon har ma da ɗan’adam.
A cikin shekaru da yawa, kuɗin cizo sun sami sauye-sauye daban-daban guda uku a cikin tsarin ƙwayoyin halittarsu wanda ke hana maganin ƙwari auka masu.
Ba mu san ainihin lokacin da waɗannan sauye-sauyen suka faru ba, amma sun kasance tun aƙalla shekarun 1950, bayan yaɗuwar amfani da sinadarin DDT a Yaƙin Duniya na Biyu.
Koyaya, har ya zuwa yanzu ba za a iya auna tasirin waɗannan sauye-sauyen a cikin ƙwarin ba.
Binciken Booth da Lewis ya nuna cewa kashi 36 cikin 100 na tsofaffin kuɗin cizon da aka tara a Amurka tsakanin 2005-2009 suna da sauyi cikin kwayar halittarsu, yayin da 50% suka sami sauyi biyu.
Kashi 2.5% na cinkinsu ba su da sauyi ko daya, don haka maganin kwari na iya tasiri a kansu.
Yaushe ne kudin cizo ke cizo?
- Kudin cizo sun fi aiki a cikin sa’o’i biyar na dare – tsakanin 12 na dare zuwa 5 na safe. Wannan ba kuskure ba ne – muna iya kasancewa a yanayin barci mai zurfi, kuma da wuya mu farka da katse musu cin abincinsu.
- Kwarin na auka wa mutane masu barci da taimakon alamu guda biyu – iskar carbon dioxide (CO2) da kuma dumin jiki. Kwarin na iya gano iskar CO2 daga nisan kafa uku, kuma sukan ji dumin jiki daga ɗan kusa da haka.
- Duk da haka, ba sai ka yi barci kusa da masaukinsu ba kafin su cije ka – kwarin na iya yawo mai nisa a cikin dare don neman wanda za su aukawa.
“Duk lokacin da aka samu ɗaya daga cikin sauyin ƙwayoyin halitta ya kan haifar da juriya da yawa kan maganin ƙwari,” in ji Booth.
“Idan aka sami guda biyu wanda zai iya kai wa zuwa ninki 16,000. Don haka, yana nufin ba za ku kashe su ba. Za ku iya zuba musu bokitin maganin ƙwari kuma ba zai yi tasiri ba.”
“Kuɗin-cizon samfurin shekarar 2018 zuwa 2019, kimanin kashi 84 na da ƙwayoyin kariya da ke kare su daga maganin feshi, don haka suna iya jurwa magani,” in ji Booth.
Ya ƙara da cewa “mafi yawan kuɗin-cizon da ake gani a wannan zamani na da irin wannan yanayi na halitta, don haka idan ka saka maganain feshi kada ka yi tunanin ka gama da su, kana buƙatar samun ingantaccen maganin ƙwari domin magance su”.
A shekarar 2018, Booth ya yi aiki da Ondřej Balvín, wani masanin ilimin halittu a jami’ar kimiyya da ke Prague a ƙasar Czech.
Sun samu damar yin nazari kan nau’ika 393 na kudin-cizo a fadin Turai, ƙasashen da aka ɗauki samfurin sun hadar da Birtaniya da Faransa da Jamus da Switzerland da Italiya da Poland da Sweden da sauransu
Wasu binciken sun nuna cewa mafi yawan kudin-cizo a Australiya da yankin Asiya ba sa rikiɗewa.
To amma bincike na baya-bayan nan ya tabbatar da cewaɗin- cizon yanzu na yawan rikiɗewa.
Kudin cizo na da ƙankanta soai ta yadda za su iya ɓuya cikin katifa ba tare da an gansu ba.
Ta yaya kudin-cizo ke cizon mutane?
- A ƙoƙarinsu na neman abincinsu, kudin cizo kan lalubo tare da nutsa bakinsu can cikin fata domin neman jijiyoyin jini, domin su tsotsi jini – wanda shi ne abincinsu, kamar yadda masu bincike a cibiyar Virginia Tech ta amurka suka bayyana.
- Kudin cizon ba sa iya samun jijiyar jinin a cizon farko, hakan na nufin wanda ake cizon zai sha wahala sosai, domin kuwa sai ƙwarin sun cije shi da yawa kafin su iya samo jini a jikinsa.
- ƙwarain kan iya ɗaukar tsawon mintuna biyar zuwa 10 kafin ƙwarin su iya huda jijiyar jinin, domin samun abincinsu.
- Bayan samun jinin da ƙwarin suka tsosa, sukan yi kimanin mako guda kafin su ƙara buƙatar abinci.