Shugabannin Musulmai sun ce laifin Ƙasashen Yamma ne ƙuncin da Gaza ke ciki
Bayani kan maƙala
- Marubuci,Daga Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari,Wakilin BBC kan harkokin tsaro a Saudiyya
- 15 Nuwamba 2023
Munafunci da baki biyu da kuma gaza fahimtar al’ummar yankin. Waɗannan na cikin zarge-zargen da shugabannin ƙasashen Larabawa da na Musulmai 57, da suka taru cikin ƙarshen makon jiya a Riyadh babban birnin Saudiyya, ke yi wa Ƙasashen Yamma, a kan gaba ita ce Amurka.
Ta yaya, ministocin ƙasashen waje suka faɗa min, Ƙasashen Yamma za su yi wa Rasha kaca-kaca saboda kisan fararen hula a Ukraine, amma kamar yadda suka ce, su “ba da dama ga Isra’ila ta aikata irin haka a Gaza”?
A katafaren zauren alfarma na otal din Ritz-Carlton na birnin Riyadh, tsakiyar manyan furanni masu ɗaukar hankali da fitilun adon saman tsakiyar ɗaki masu sheƙi, wata duniya nesa daga ruguje-rugujen bam na Gaza, inda ‘ya’yan sarauta da shugabannin ƙasashe da firaministoci suka haɗu don Taron Ƙolin Haɗin Gwiwar Ƙasashen Larabawa da na Musulmai.
Alhakin yaki da kashe-kashen rayuka da rugurguza dukiya kacokam an dora wa kasar Isra’ila da magoya bayanta. Babu wani da ya soki lamirin Hamas kan samamen da ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba a kudancin Isra’ila wanda ya yi sanadin kashe mutum 1,200, da kuma yin garkuwa da karin wasu 240, lamarin da ya haddasa gagarumin matakin soja. Isra’ila dai ta ce babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa, ya aikata miyagun laifuka.
“Muna gargadi kan sakamako na bala’i kan auka wa Zirin Gaza da yakin ramuwa daga Isra’ila, wanda ya yi daidai da aikata laifin yaki,” a cewar sanarwar bayan taro. “Muna gargadi kan hatsarin gaske na bazuwar yakin sakamakon kin yardar Isra’ila na dakatar da takalar fadanta da gazawar Kwamitin Sullhu na Majalisar Dinkin Duniya wajen tilasta aiki da dokar kasashen duniya don kawo karshen wannan takalar fada.”
Mutane kalilan da na zanta da su a taron, suka yi tsammanin Isra’ila za ta wani kula. Maimakon haka, a bayyane take cewa wannan taro da sakon da yake niyyar isarwa na hadin kai zai nufi babbar mai goyon bayan Isra’ila ne – Amurka.
Shugabanni na son gwamnatin Biden da Kasashen Yamma gaba daya su sa isasshen matsin lamba a kan Isra’ila don ta dakatar da yakin kwata-kwata.
Sai dai abin da ba su iya amincewa a kai ba, shi ne yadda za su cimma hakan.
Taron kolin ya tattara wasu kasashe wadanda ba sa shan inuwa daya – wata alama da ke nuna damuwar da yankin ke da ita, game da yiwuwar tabarbarewar abubuwan da ke faruwa a Gaza, har su fi karfinsu.
Iran – babbar abokiyar gabar Isra’ila – ta halarta, inda Shugaba Ebrahim Raisi ya yi tattaki a kan dardumar da aka shimfiɗa a faɗin zauren, cikin baƙar alkyabbarsa ta malamai, jami’an tsaro fuskoki a murtuke sanye da baƙaƙen kwat, wasu da shat maras kwala, suna rufa masa baya. Wannan shi kansa, abu ne mai ban mamakin gani.
Kafin ɗinke ɓarakar bambance-bambancensu a watan Maris ɗin wannan shekara, Saudiyya da Iran, manyan abokan gaba ne da ke musayar baƙaƙen kalamai masu cike da zarge-zarge. Har yanzu suna da manufofi masu cin karo da na juna, inda Iran take goyon bayan abin da wasu da yawa ke kira “sojojin sa-kai ‘yan barandanta” – kamar Hamas a Gaza da Hezbollah a Lebanon da kuma ‘yan Houthi a Yemen.
‘Yan Saudiyya, tare da Larabawa abokan ƙawancensu masu ra’ayin ‘yan mazan jiya kamar Masar da Jordan, na kallon waɗannan ƙungiyoyi a matsayin masu hatsarin hargitsa al’amura.
Da yake baro filin jirgin saman Tehran zuwa Riyadh, Shugaba Raisi ya ce yanzu lokaci ne na ɗaukar mataki a kan Gaza, ba magana ta fatar baki ba.
Sai dai duk wanda ya zo yana sa ran ganin an ɗauki ƙwararan matakan hukunci a kan Amurka da Birtaniya, ya koma ɓacin rai.Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahrain, waɗanda a kwanan nan ne kawai suka ƙulla cikakkiyar hulɗar ciniki da diflomasiyya da kuma tsaro a ƙarƙashin Yarjejeniyar Abraham, sun bijirewa kiraye-kirayen katse su.
Shi ma Shugaban Siriya Bashar al-Assad ya je taron. Kafin wani lokaci a baya-bayan nan, ya kasance saniyar ware a tsakanin ƙasashen Larabawa saboda matakan murƙushewa da gwamnatinsa ta yi amfani da su a yaƙin basasar Siriya.
Ya faɗa wa taron cewa ba zai tsinana abin a-zo-a-gani ba, matuƙar ba su ɗauki ƙwararan matakai ba, sannan shawarwarin sanya takunkumin sayar da man fetur ko tashin sansanonin sojin Amurka daga ƙasashen Larabawa, ba tare da wani ɗaga murya ba, aka gwale su.
- Ƙasashen Musulmi sun fusata da ƙona Alƙur’ani a Sweden29 Yuni 2023
- Masu ikirarin jihadi ‘sun fi kashe Musulmi a duniya’16 Janairu 2020
- Me wasikar da Saddam ya rubuta wa Falasɗinawa kafin kashe shi ta kunsa?26 Oktoba 2023
Duk da haka, babu wani musu cewa samamen da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba da kuma yaƙin da ya kaure sun canza gaba ɗayan alƙibla a Gabas ta Tsakiya. Can kafin safiyar ranar mai cike da kashe-kashe a kudancin Isra’ila ginshiƙan siyasar yankin Gabas ta Tsakiya na juya baya ne ga muradan Iran da sojojin haya abokan ƙawancenta
Kasashen Larabawa shida tuni sun ƙulla cikakkiyar dangantaka da Isra’ila, Saudiyya ma ta kama hanya gadan-gadan don yin hakan. Ministan harkokin yawon buɗe ido na Isra’ila ya kai ziyara birnin Riyadh, kwanaki ƙalilan kafin harin Hamas. Dubai tana ta jan hankali ɗumbin ‘yan Isra’ila masu yawon buɗe ido, ga kuma gagarumar yunwar da Larabawa ke da ita, ga kayayyakin ƙwarewa na Isra’ila a fannin fasaha da ƙere-ƙeren bin ƙwaƙƙwafi da fasahohin inganta rayuwa da kuma sauran fannoni.
Idan an cire Qatar, wadda ke karɓar baƙuncin shugabannin Hamas, shugabannin Larabawa na yankin Gulf sun gaji da abin da suke gani a matsayin cin hanci da rashin iya tafi da al’amura da kuma rikicin cikin gida na shugabancin Falasɗinawa.
Ko da yake suna tausaya wa halin ƙuncin rayuwa na jama’ar Falasɗinawa, waɗanda ba su da ƙasa bayan kwashe tsawon shekara 75, amma galibi suna ganin cewa Isra’ila a matsayinta na ƙasa, na da ɗumbin muhimmancin da ta fi ƙarfin a yi babu ita, kuma lokaci ya yi da za a yunƙura, a daidaita alaƙa da ita. Maganar makomar ƙasar Falasɗinu, ko da yake har yanzu ana jin amonta a cikin jawabai, amma tana samun kulawa ‘yar kaɗan a aikace.
A yau, dangantaka tsakanin waɗannan Larabawa da Isra’ila, duk da har yanzu ba ta karye ba, amma tabbas tana sukurkucewa a gefe.
“Gaskiya muna cikin damuwa game da ƙeƙashewar matasanmu,” ɗaya daga cikin ministocin ƙasashen Larabawa ya faɗa min a bayan fage. “Suna kallon abin da ke faruwa a Gaza a talbijin kuma suna daɗa fusata.”
Na sha jin yadda mahalarta taron ke guna-gunin cewa matakan da gwamnatin Netanyahu ke ɗauka sun zarce batun kare-kai, kuma ayanzu yana jan yankin gaba ɗaya zuwa wata gangara mai hatsari. Ana nuna damuwar cewa bayanan da masu tsattsauran ra’ayi ke yaɗawa, suna ƙaraa samun tagomashi a intanet.
Shugabannin ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun fusata kan yadda Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gaza a idonsu, wajen tabbatar da ganin sojojin Isra’ila suna taka-tsantsan a Gaza. Adawar da Amurka ke nunawa ga kiraye-kirayen tsagaita wuta, ya yi matuƙar bai wa ƙasashen da take kira abokan ƙawancenta a yankin, kunya.
Muhimmin ƙawancen gwamnatin Washington da ƙasashen Larabawa masu arziƙin man fetur a yankin Gulf, ya faro ne tun a 1945, da wata ganawa a lokacin yaƙi a kan jirgin ruwan sojin Amurka a Tekun Maliya, tsakanin Shugaba Eisenhower da kuma mutumin da ya kafa ƙasar Saudiyya ta wannan zamani, Sarki Abdulaziz. A yau, Amurka har yanzu tana samar da ɗumbin harkokin tsaron ƙasa da Saudiyya da Larabawan yankin Gulf suke buƙata.
Sai dai a ƙarƙashin ƙasa, abubuwa suna canzawa. Tun lokacin da gwamnatin Obama ta ɓullo da tsarin “karkata zuwa Asiya”, akwai wata fargaba a nan cikin Gulf, cewa muradin Amurka a yankin yana raguwa, kuma ba za a iya ci gaba da dogaro da ita a matsayin wata abokiyar ƙawance mai riƙe alƙawari ba.
A lokaci guda, ƙarfin faɗa-a-jin Moscow da Beijing yana ƙaruwa. China a baya-bayan nan ce ta shiga tsakani don ganin Iran da Saudiyya sun mayar da alaƙa. Putin ya burge shugabannin Larabawa da goyon baya maras iyaka da ya bai wa Shugaba Assad na Siriya. Suna kwatanta wannan, da yadda cikin gaggawa Washington ta yi watsi da Shugaba Mubarak na Masar a 2011, lokacin da cincirindon mutane suka fita zanga-zanga a Dandalin Tahrir na birnin Alƙahira.
Duk waɗannan, ba wai suna nuna cewa Ƙasashen Yamma sun rasa abokan ƙawancensu ba ne a Gabas ta Tsakiya. Larabawa abokan ƙawancen Yamma ƙarara sun ƙi yin wani abu da ya zarce kalaman fatar baki a kan Washington. Saboda suna so a saurare su, kuma a dakatar da tashin hankalin da ke faruwa a Gaza yanzu, kafin al’amura a yankin da ma ƙasashensu, su taɓarɓare har su fi ƙarfinsu.