CLOUD COMPUTING A TAKAICE(BA GAJIMARE BANE, NA’URA NE

CLOUD COMPUTING A TAKAICE(BA GAJIMARE BANE, NA’URA NE)

Kasacenwar yanzu duniya kullum

cigaba ake, abubuwan fasaha kuwa sai kara bayyana suke, daya daga cikin ire iren wadannan abubuwa da suke tashe a yanzu shine “CLOUD COMPUTING”. Wannan fasahar abune mai kyau da tsari wanda ke taimakawa kamfanoni, kasuwanci da sauransu. Kuma ga daliban da suke karatun Computer Science da kuma dukkan wani fanni da ya dangance Computar, wannan bayanin zai taimaka wajen kara fahimtar abin.

MENENE CLOUD COMPUTING?
Cloud Computing fasaha ce da aka fitar dashi domin ragewa kamfanoni, ma’aikatu, makarantu da masana’antu kudin da suke kashewa a yayin kulada “Servern” shafukansu ko manhajojinsu. Kamfanonin da suke samar da fasahar Cloud Computing sukan samarwa abokanan huldarsu fasahohi kamar “Servers, Storage (Rumbu), databases (Rumbun ajiye bayani), networking, analytics (Kididdiga game da shafukansu ko manhaja) da sauransu” ta hanyar amfani da yanar gizo. Cloud Computing tamkar da Server da muke amfani dasu yau da kullum ne, ma’ana wadanda muke hosting din Website dinmu idan muke kalleta ta fuskar ganuwa, sai dai kuma akwai banbanci sakaninsu nesa ba kusa ba, domin Cloud Computing tamkar Servernka na kanka (Physical Server) ma’ana misali, idan muka dubi kamfanoni da masana’antu zamu ga cewar suna kashe makudan kudade wajen Siyan Server (Rack) wanda zasuyi amfani dashi don ajiye shafukan yanar gizo ko manhajoji, sannan zasu nemo masu kulada shi, haka suna bukatar wadanda zasu kulada tsaron bayanansu da zasu ajiye kuma dole su biya duka wadannan abubuwan. Shi kuwa CLOUD COMPUTING yana dauke da dukkan wadannan abubuwane acikinsa, domin idan har kafara aiki dashi kai zaka zabi Yanayin Server da kake bukata, Operating System dinda kakeso yayi aiki akan Servern da sauransu kuma baka bukatar ace kasiyo su Rack da sauransu, domin kuwa duk wani abu da ya danganci Tsaron bayanai, kula da servern da sauransu da matsalolinsu kamfanin da kasiyi plan din Cloud Computing din su sune zasu kula dashi.

Haka kuma wani daga cikin babban amfanin cloud computing shine sauri domin kamfanoni da suke bada fasahar Cloud Computing sunada “Data Center (Matattarar Bayanai) manya masu dauke da miliyoyin Server” sabanin Servern da mutun zai siya sannan yarinka mar hidima kuma idan visitor sukayi yawa yayi nauyi. Sannan Cloud Computing suna dauke da hanyoyin da zasu sauwake dukkan wahala da mutun zaisha wajen yin wasu abubuwa a Server misali, hanyar da mutun zaibi wajen yin notification irin WhatsApp, na tabbata idan mutun ne zaiyi da kansa yana bukatar abubuwa diyawa kuma zaisha wahala amma ta hanyar amfani da Cloud Services irinsu Google Cloud Computing nanda nan mutun zai hada irin wannan notification din domin kawai wasu functions ne mutun zai rubuta acikin code dinsa shikenan yagama.

SANANNU DAGA CIKIN CLOUD COMPUTING KAMFANI

  1. AWS (AMAZON WEB SERVICES)
  2. MICROSOFT AZURE
  3. CLOUDFLARE
  4. GOOGLE CLOUD COMPUTING
  5. Digital Occean
    da sauransu. Wadannan sune manya kuma sanannu sai dai kowane yanada wani alfanu da yafi wani kuma kowane akwai inda ya dace ayi amfani dashi, misali CloudFlare kashi 70% na abubuwan suke samarwa tsaro ne wato (Security).

WASU DAGA CIKIN ALFANUN CLOUD COMPUTING

IRE IREN CLOUD COMPUTING

KARKASUWAN ABUBUWAN DA KAMFANONIN CLOUD COMPUTING KE SAMARWA
Mafi yawan abubuwan da Cloud Computing Services ke samar suna cikin guda hudun nan

Exit mobile version