Kafin a yi updating manhajar Xender, wajajen 2015/2016, akwai wajen da zai nuna maka “Create Group”, idan ka danna zai bude group ya ba wa abokanka damar sharing files a tsakaninku. Yanzu duk files din da ka tura musu, dukkansu za su yi receiving. Sannan idan daya daga cikinsu ya tura, dukkanku za ku yi receiving (idan ban manta ba).
To haka “internet” take! Da farko, internet yana nufin interconnected networks. Shi kuma networking yana nufin hadakayyar na’urori, kamar dai na Xender, tun da sun yi connecting da juna to sun samar da network kenan.
—An fara samun basirar samar da internet ta hanyar samar da Local Area Network (LAN), wanda yake hadakayyar na’urori ne wadanda suke wuri guda (suke kusa da juna) a wani building guda, ko makaranta, ko asibiti, ko kamfani da sauransu. Wadannan computers din za su yi connecting da juna su yi sharing information.
—Daga nan aka matsa zuwa Metropolitan Arewa Network (MAN) wanda ya kasance cigaban na baya, wato yanzu an samu cewa computers za su iya connecting ko kuma a iya sharing information a gari guda, ko yanki guda. Misali kamar radio.
—A hankali aka samu cigaba zuwa Wide Area Network (WAN), wanda ya kasance cigaban da zai iya hada computers a kasa guda ko kuma nahiya sukutum, misali Africa, don su yi connecting da juna ko sharing information.
Daga WAN, sai aka ce bari a hada nahiyoyi biyu zuwa uku, misali tunda yanzu a Yobe ko Arewa ko Nigeria gabadaya an samu connection guda, sannan a Africa an samu WAN, to me zai hana mu hada connection dinmu da nahiyar Asia, da Europe, da North America da sauransu?
Haka aka yi. Amma domin a hada wadannan nahiyoyi, akwai nisa tsakaninmu kuma wasu lokutan sai an tsallake teku (oceans), sai aka samar da wata waya (wire) mai suna fiber optic cable wacce aka shimfida ta a kasan teku don ta kai connection wadannan nahiyoyin.
Fiber optic cable ta hada wadannan nahiyoyin, su kuma nahiyoyin daman sun hada kasashen da ke cikinsu. Daman ko a cikin nahiyoyin, sun yi amfani da fiber optic cable din wajen connecting kasashensu.
Yanzu mun fahimci cewa network of networks shi ne internet — interconnected networks kenan.
Bari in tsaya a nan in ga ko an fahimta…
16th September 2024