
Menene Satellite Imagery?
Fasaha ce da zata taimaki kasarmu a iya gane me yake faruwa a wani wuri mai nisa ko a cikin duka dajukan dake Nigeria.
–Zata taimaka wurin gano asalin wurin da yan ta’adda suke boyewa.
–Zata taimaka wurin tracking na duk motsin yan ta’adda da suke a daji.
–Duk wani abu da yake a gabadaya zagayen nigeria, da duka dajukan dake nigeria za’a iya ganinsa.
–Zata taimaka wurin fahimtar yadda duka dajukan Nigeria suke.
Shin taya zamu iya amfani da wannan fasahar a Nigeria?
- Nigeria zatayi Partnership da satellite company saboda ta samu access na images din da ake son samu dake cikin dajukan kasar.
- Bayan an samu anyi Partnership sai a samu wata Special software wacce za’a dinga analyzing na Images din da aka samu a dajukan.
- A koyar da jami’an tsaro yadda fasahar take aiki, da yadda zasu iya interpreting na images din.
- Lallai a samar da Monitoring Center, wacce zata zama tana monitoring duk wasu dajuka dake cikin Nigeria.
- Za’a kashe a kalla 1.3 Billion wurin samar da komai da komai na wannan fasahar harda Monitoring Center.
- Bayan an samu Information na dajukan da yan’ta’addan suke sai a tura ma jami’an sojan kasa Information na Exactly location na dajukan da yan’taddan suke, sai su kuma suyi kwanton bauna, su karar dasu duka.
Shikenan, an kammala da barayin daji.😀
Jira Jira Jira! Kai Saheel a Nigeria kake bamusan hauka, idan an kashe yan daji ba’a kashe masu daukar nauyinsu ba, me kenan akayi? Shirme kenan.
This Is Nigeria.