Yadda Ake sentimental analysis


.
.
Today’s FEAR and GREED index is GREED.

∆ Yau Bari nayi muku bayani akan Me ake nufi dashi wannan “FEAR AND GREED INDEX” ɗin!?

∆ Sannan wane irin labari yake bamu a kasuwa!?

∆ Sannan kuma taya ne muke Amfani dashi.

Analist
img 20241123 wa0007

Muje zuwa..

“FEAR AND GREED INDEX”: Shine ma’aunin da muke Amfani dashi wajan fahimtar halin da mutane suke ciki a kasuwa.
Halin “TSORO (FEAR)” ko kuma “HAƊAMA (GREED)”.
Da wannan ne muke fahimtar ina kasuwa zata dosa.
Kuma shi wannan tsarin muna kiran shi da: “SENTIMENT ANALYSIS”.

A ƙa’idar ko wace kasuwa, idan har kaga mutane suna cikin halin (“TSORO” FEAR) To sunga wasu sun tafka Babbar Asara ne a cikin kasuwa, ko kuma maybe a irin wannan lokacin sun fahimci cewa kasuwa tana faɗuwa sosai.
wanda hakan shine zai saka su cikin tsoro har su dinga cire kuɗin su daga kasuwa, ko kuma suƙi saka kuɗin su a cikin kasuwa.
Wannan matakin da suke ɗauka shine yake jawo faɗuwar farashin kaya a cikin kasuwa. Domin “SUPPLY” Yana ƙaruwa, Amman kuma Babu “DEMAND”.

To a wannan lokacin su kuma wanda suka san Kasuwa sosai kuma suka jima a kasuwa, suna siyan wannan kayayyakin ne su ɓoye saboda a wannan lokacin farashi yayi sauƙi (ASSET IS CHEAP).

A lokacin da kasuwa ta shiga yanayi na HAƊAMA (GREED) kuma, to ana samun kowa yana ɗauko kuɗin sa ne ya zuba a cikin kasuwa. Saboda yaga mutane da yawa sunci riba, maybe yaga wani ya sayi kayan 1 million, ya samu ribar 100 million. Kaga yaga zahiri ana cin riba a kasuwa.
A wannan lokaci shima zai yi gaggawa ya ɗauko kuɗin sa ya zuba a kasuwa, domin shima ya samu irin wannan ribar.
A irin wannan lokacin ne zaka ga wanda ba harkar yake Bama zaka ga ya ɗauko kuɗin sa ya siyi wannan kayan, saboda yaji labarin wani ya samu ribar kuɗaɗe masu yawa.

To haka wannan tsarin yake a dukkan “Financial Markets” Ciki harda kasuwar CRYPTOCURRENCY. Wanda a ita ne ma muke magana yanzu.

Shehin malamin kasuwar hannun jari(STOCK MARKET) me suna “Warren buffett” yayi wani “QUOTE” me ma’ana, inda yace:

“BUY WHEN PEOPLE ARE IN FEARFUL.
And
SELL WHEN PEOPLE ARE IN GREEDY”.

Tsarin yadda muke aiki da shi wannan INDEX ɗin shine:
The Ratio is from 0-100.

From 0-25 = Extreme Fear 😨: Hakan yana nuni da cewa kowa yana cikin matsanancin Tsoro a kasuwar Crypto. (Wanda a yadda WARREN BUFFETT yace wannan ne lokacin daya kamata kai kuma ka zama GREEDY, ma’ana Ka kwaso kuɗi ka siya).

From 26 – 49 = FEAR Hakan yana nuni da cewa Al’umma suna cikin tsoro, Amman kuma ba matsananci ba. Wanda shima lokaci ne me kyau daya kamata ka kafa kanka a kasuwa!.

From 50-59 = NEUTRAL (Hakan yana nuni cewa kasuwa tana tsaka tsaki, Al’umma basa cikin tsoro, kuma basu fara haɗama ba).

From 60 – 70 = GREED (Hakan yana nuni da cewa Al’umma sun fara shiga haɗama, A lokacin ne, kowa yake zuwa yake shiga saboda ya samu labarin ai Wasu sun samu 10× 5×, wannan wanda suka samu 10× ɗinnan sune suka shiga tun lokacin da “SENTIMENT” ɗin yake a nuna musu “EXTREME FEAR” lokacin da farashi yayi rugu rugu, saboda Supply yayi yawa a Kasuwa. (A bayanin “WARREN BUFFETT” wannan lokacin shine lokacin jin tsoro. Lokacin da kowa yake cikin Haɗama)

From 71-100 = EXTREME GREED (Hakan yana nuni da cewa An shiga matsananciyar Haɗama! Kowa zuwa yake ya siya kawai, (wanda bai san yadda ake siya ko SIYAR da crypto Bama, ya ɗauko kuɗin shi yace a siya masa, saboda labari daya samu na wanda suka siya a lokacin da kasuwar take “FEAR” Suma sun samu 5× 100×.

Domin kallon Wannan INDEX ɗin.
Ga Wannan channel ɗin suna saka wannan Index ɗin kullum. Zaku iya Bibiyar su:
(Link a comment section).
ko kuma ku dinga duba (Coinmarket cap, COIN GECKO, CRYPTO RANK.IO) duka zaku dinga samun su anan.

Ko kuma kan Story na na Facebook, ina ɗorawa kullum.

NOTE: Banda wannan INDEX ɗin, akwai abubuwa da yawa da muke kalla wajan fuskantar wannan SENTIMENT ɗin(wanda nayi Video akai a ciki YouTube channel).

Allah ya bada sa’a

Idan ka ƙaru kayi sharing zuwa gaba domin wasu ma su Amfana!

Exit mobile version